Snack's 1967

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From start
* ibnhujjah HIKIMAR YAWAITA AZUMIN NAFILA A CIKIN WATAN SHA’ABAN
Manzon Allah (SAW) ya bayyana dalili da hikimar yawaita azumi a cikin watan Sha’aban. Hikimonin sune:
1. Watane da mutane suke gafala da shi wurin azumi da sauran Ibada, a tsakanin watan Rajab da Ramadan.
2. A cikin watanne ake daukaka ayyukan bayi zuwa ga Allah.
3. Wannan watan ne Allah yake yin gafara ga bayin sa a cikin rabin Sha’aban.
Duka Manzon Allah (SAW) ya bayyana wadannan hikimomi a hadisai kamar yadda ya gabata a darasin farko.
Imam Ibn Rajab yana cewa:
“Yawaita azumi a watan Sha’aban kamar gwaji ne da training don shiga azumin Ramadan, don kada mutum ya shiga Ramadan ya sami tsanantuwar azumi a gare shi, amma idan aka gabatar da training a wannan watan sai jikin mutum ya saba kafin shigar Ramadan. Kasancewar watan Sha’aban shi yake gabata kafin Ramadan, sai aka shar’anta maka yawaita azumin nafila a cikin sa da karatun alqur’ani da sauran ibada don shiri da kimtsin shiga watan Ramadan, don mutum ya shiga watan Ramadan yana mai nishadi da son yawaita ibada da biyayya ga Allah mai Rahama.” [Duba littafin Lata’ifil Ma’arif na Ibn Rajab, shafi na 138]
Wassalamu AlaikumWassalamu Alaikum. << Kucigaba Da Kasancewa, Da islamicforum.com.ng A Koda Yaushe .>>
2018-04-18 13:31 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 178 user
This Week : 776 user
This Month : 777 user
Total all : 94184 visitorsUnited States
LAST PAGES