XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From start
Aliyu Haruna * ibnhujjah Mungode
2018-02-06 03:16 · Reply · (0)
* ibnhujjah ME YASA AKE KAFIRTA 'YAN SHIA ?
Tambaya :
Assalamu alaikum, ina yiwa malam fatan alkairi,
Allah ya hadamu a Aljannar da koramu suke gudana
a cikinsa, tambayata shi ne: Don Allah malam
wanne abubuwa ne wanda 'yan Shi'a suke aikatawa
wanda ya fitar da su daga musulunci ?
Amsa:
To dan'uwa tabbas a cikin addinin shi'a akwai
manyan abubuwa wadanda suke warware
musulunci:
1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai,
tare da cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da
su a ayoyi da yawa a cikin alqu'ani, duk wanda ya
ce mafi yawancin sahabban Annabi s.a.w. sun
kafirta tabbas ya karyata Allah, wanda ya karyata
Ubangiji hukuncinsa a fili yake.
2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa :
Alqur'anin da yake hannunmu bai cika ba, tare da
cewa : Allah ya tabbatar : zai kiyaye shi, har abada.
3.Suna riya cewa : an yi kuskure wajan baiwa
Annabi S.a.w. Annabta, sayyadi Aliyu ya kamata a
bawa, sai mala'ika Jibrilu ya yi kuskure ya bawa
Annabi Muhammad S.a.w, tabbas wannan maganar
ta kunshi nuna gajiyawar Allah da kuma karyata shi.
4.Rafidha 'yan shia sun tafi akan cewa Nana A'isha
Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita
daga abin da munafukai suka zarge ta da shi a
ayoyi guda goma a suratun Nur.
Ba duk mutumin da ya riya abubuwan da suka
gabata ba za'a kira shi da kafiri, dole sai an
tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba
shi da wata Shubha wacce ta kasa warwaruwa.
Yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman
AHLUSSUNNAH ba duk wanda ya aikata kafirci ake
cewa kafiri ba, don haka jahilai a cikin 'yan shi'a da
gama-gari wadanda suka shiga shi'a saboda talauci
ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu
kafirata su ba, ko da kuwa suna riya wadancan
abubuwa da suka gabata, saboda akwai hadisai da
yawa wadanda suke bawa wanda ya aikata kafirci
da jahilci uzuri, amma wanda ya aikata daya daga
cikin su da ilimi to malaman musulunci da yawa
sun dora masa KAULASAN.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba: Ashshifa'a Na Kadhi
IYadh 26 da Al-kifaya :67
Dr. Jamilu Zarewa
2415
2017-12-24 03:02 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 208 user
This Week : 806 user
This Month : 807 user
Total all : 94214 visitorsUnited States
LAST PAGES