XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

* ibnhujjah JAMA'AR NIGERIA SAI MU KARA GODE WA ALLAH:
1. Wajibi ne mu al'ummar Nigeria mu kara gode wa Allah saboda irin yadda Ya kawar mana da barazanar da muka fiskanta daga 'yan ta'addan Bokoharam ta share kasancewar wata kasa da ake kira Nigeria a doron Duniya.
2. Lalle wajibi ne mu al'ummar Nigeria mu kara gode wa Allah a kan wannan Ni'ima ta kauda barazanar Bokoharam; sannan kuma wajibi ne mu jinjina wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda irin kyakkyawan jagorancin da ya nuna har aka sami kai wa ga irin wannan nasara.
3. Sannan abu ne da ya dace dukkan 'yan kasa na gari su kara kaskantar da kai a gaban Allah su roke Shi domin Ya taimaki al'ummar Nigeria, Ya ba wa Shugaban Kasa nasarar kauda dukkan fitinun da gurbatattun 'yan kasa ke kunnawa a cikin wannan Kasa tamu; gurbatattun 'yan Kasa kamar kungiyar CAN, da masu fashin shanu, da masu garkuwa da mutane, da masu fashi da makami, da kungiyoyin asiri, da kungiyoyin tarzoma, da gurbatattun 'yan siyasa.
Allah Ka tausaya wa al'ummar Nigeria Ka sanya ta cikin bayinKa masu gode maKa a kan ni'imominKa. Ameen.
2018-07-08 12:24 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 10 user
This Week : 608 user
This Month : 609 user
Total all : 94016 visitorsUnited States
LAST PAGES