Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From start
* ibnhujjah SAKO ZUWA GA KUNGIYAR C.A.N:
1. Muna gaya wa kungiyar CAN cewa: tunda dai a Nigeria ne take, to kuwa dole ne ta lazimci yin aiki da Constitution din Nigeria, hakan ya yi mata dadi, ko kuwa bai yi mata dadi ba, hakan ya dace da abin da Kiristanci yake so, ko kuwa bai dace da abin da Kiristanci ke so ba.
2. Sannan yana da kyau kungiyar CAN ta san cewa: tunda dai addinin Kirista shi ne addininta; addinin da ginshikinsa shi ne: yarda da cewa Allah na ukun uku ne. Da yarada da cewa Jesus Allah ne, kuma dan Allah ne. Da yarda da cewa wata diya mace ce ta haifi Allah, kuma Allan da yake cin abinci, yake kuma shan ruwa, yake kuma yin barci, yake kuma zagayawa bayan gida, yake kuma yin kuka saboda jin zafi da bakin ciki, yake kuma mutuwa har na tsawon kwana uku, yake kuma siffantuwa da wasu siffofi masu kama da wadanda ambaton su ya gabata; muddin dai wannan shi ne ginshikin addinin Kirista, to kuwa dole ne ita kungiyar CAN ta kara shirya wa ganin kiristoci masu fita daga irin wannan addinin daga lokaci zuwa lokaci, suna komawa zuwa ga addinin Musulunci; addinin kadaita Allah tare da kadaita shi da bauta.
3. Har yanzu yana da kyau kungiyar CAN ta san cewa: a kasashen Turai, da America, ba ma Kiristoci musulunta ba ne kadai suke yi, a'a har ma Coci-cocinsu ne suke sayar wa Musulmi domin a maida su Masallatai.
4. Sannan Yana da kyau kungiyar CAN ta tuna da cewa: mu a nan Jihar Taraba kiristoci a matakai na addini daban-daban ne suke ta shiga Musulunci a kullum; bishop na musulunta, reverent na musulunta, maza na musulunta, mata na musulunta, kuma har gidajen Malaman Musulunci ne suke zuwa domin su musulunta, kuma wannan musuluntar da suke yi dama ce da constitution din Nigeria ya ba su, babu kuma mai yin kokarin hana su wannan damar ta hanyar yin amfani da bata-gari cikin 'yann sanda, da alkalai sai makiya Nigeria, sai makiya Constitution din Nigeria.
5. Allah muke roko da ya taimake mu, ya raba mu da sharrin kungiyoyin tarzoma a cikin kasarmu Nigeria. Ameen.
2018-06-24 13:56 · Reply · (0)

Online: Guests: 2

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 52 user
This Week : 650 user
This Month : 651 user
Total all : 94058 visitorsUnited States
LAST PAGES

Ring ring