Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *_SHIN ZAMU IYA YIN WANKA DA RUWAN ZAMZAM?_*
*Tambaya*
Shin Malam zamu iya yin wanka da Ruwan Zam-Zam?
*Amsa*
To dan’uwa ruwan Zam-Zam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami’ussagir, duba Faidhu Alkadeer 3/489.
Saidai duk da haka ya halatta ayi wanka da tsarki da shi a zance mafi inganci, saboda ba’a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin ka’idojin malamai duk abin da ba’a samu nassin hani akansa ba a cikin mu’amalolin mutane, to ya halatta.
Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo daga hannun Annabi S.A.W, ruwan Zam-Zam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba.
Don neman Karin bayani duba: Hashiyatu Ibnu-abiidin 10 da kuma Insaf 1.
Allah ne mafi Sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
2018-07-10 20:40 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 159 user
This Week : 475 user
This Month : 475 user
Total all : 96281 visitorsUnited States
LAST PAGES

Snack's 1967