Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah YAN SHI'AH SUNA YI WA MANZON ALLAH KARYA:
1. Lalle 'yan shi'ar da suke girmama mamuguntan Kungiyar CAN, suke zuwa coci-cocinsu suna nuna farin ciki da murnar sauraron ire-iren kafircinsu na irin yadda suke yi wa Allah karya na cewa Almasihu Allah ne, ko dan Allah ne, ko na ukun Allolo uku ne; kuma yan shi'an suna yin hakan ne a matsayin addini suke yi, a matsayin cewa haka Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi da kiristocin zamaninsa; lalle wadannan yan shi'ah sun kara zama batattu a idanun Shari'ah; saboda wannan kage, da yarfe da suke yi wa Annabi mai tsira da amincin Allah, da kuma addinin Musulunci.
2. Tabbas babu inda Annabi mai tsira da amincin Allah ya taba shiga cocin kiristoci a matsayin ibada, ko zumincin da ake neman lada da shi a gurin Allah Madaukaki.
3. Gaskiyan al'amari ma shi ne kiristocin zamanin Manzon Allah sun yake shi a lokacin da yake raye, shi ma kuma ya yake su. Domin tabbatar da wannan magana tamu ga misalai kamar haka:-
- a shekarar Hijira ta 5 a watan Rabi'ul Awwal Annabi mai tsira da amincin Allah ya yaki kiristocin Banu Qudhaa'ah da Banu Gassan daga Daumatul Jandal.
- a shekarar Hijira ta 6 a watan Sha'aban Annabi mai tsira da amincin Allah ya yaki kiristocin Banu Kalb har yanzu a Daumatul Jandal.
- har yanzu a zamanin da Annabi mai tsira da amincin Allah yake raye Musulmi sun yi yaki da kiristoci a Zaatu Atlah da ke cikin Kasar Sham.
- uwa-uba ma mash'hurin yakin nan na Tabuka da Annabi mai tsira da amincin Allah ya jagoranta a shekarar Hijira ta 9 yaki ne da daular kiristoci watau daular Rumawa Bizantawa.
4. Yana da kyau a san cewa a Musulunce ba a siffanta Najaashiy Sarkin Habasha da cewa shi Kirista ne, a'a abin da ake cewa shi ne: Najaashiy Sarkin Habasha Musulmi ne da ya mutu a cikin Musulunci, amma kafin ya musulunta shi Kirista ne.
5. Yana da kyau yan shi'ah su san cewa ba a bauta wa Allah ta hanyar jahilci, da son zuciya.
Allah muke roko da Ya shiryar da al'ummarmu. Ameen.
2018-04-27 21:50 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 44 user
This Week : 432 user
This Month : 433 user
Total all : 93840 visitors
LAST PAGES

Ring ring