Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From start
* ibnhujjah ZAKKAR KONO
1. Zakkar kono ko fidda-kai sadaka ce da ta wajaba akan musulmi sakamakon shan ruwa daga azumin Ramadan.
2. Manufarta na komawa ga tsarkake musulmi daga abubuwan da ya yi na sakaci, sakin baki da kwarkwasa a cikin kwanakin azumin Ramadan.
3. Haka nan kuma hanya ce ta ciyar da mabuqata, da taimakekeniya tsakanin musulmai da kuma gode wa ni’imar Allah ta ganin karshen azumi lafiya da wadata.
4. Zakkar kono wajibi ce akan dukkan musulmi wanda ke da halin fid da ta.
5. Mutum zai fitar wa dukkan mutanen da ke qarqashin ikonsa )matan aure, ‘ya’ya, marayu, barori da sauran wadanda mutum ke ciyar da su(.
6. Mutum zai fitar wa iyayensa idan shi ke daukar dawainiyarsu.
7. Hakanan za a fitar wa wanda ya riski azumi ko da ba ya nan a lokacin fitarwar )kamar wanda yai tafiya ko ya rasu cikin watan azumin(.
8. Miji zai fitar wa matarsa wacce ke iddar saki matuqar iddar ta shiga cikin watan Ramadan.
9. An samo daga wasu magabata kamar Uthman B. Affan )( suna fitar wa dan da ke ciki.
10. Ana iya fara fitar da zakkar kono da zaran an yi azumi daya.
11. Amma ba za a bai wa mabuqatan ba sai gab da sallah )kamar kwana guda ko biyu(.
12. Yana daga cikin tafarkin Sunna ya zam akwai amintattun da za su dinga tara zakkar da raba ta ga wadanda suka cancanta a lokacin da ya dace.
13. Ana fitar da sa’ee guda ne ga duk mutum guda.
14. Malamai suna qiyasin sa’ee da cewa yana daidai da tafi hudu na matsakaicin mutum.
15. Ko za a iya qimanta kudin zakkar fidda-kai a bayar a maimakon abincin? Ibn Qudamatal Maqdisiy da Bin Baaz )( sun ce bai dace ba.
16. Wanda duk ya bari har aka dawo idi bai fidda zakkar kononsa ba ya yi laifi matukar ba yana da uzuri mai qarfi ba.
17. Wajibi ne ya tuba sannan kuma ya fitar da ita a matsayin sadaka gama-gari.
18. Allah shine mafi sani.
ALLAH YA KARBA, ALLAH YA SA MU DACE
2018-06-14 04:58 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 375 user
This Week : 973 user
This Month : 974 user
Total all : 94381 visitorsUnited States
LAST PAGES

Polly po-cket