ibnhujjah
1. Wajibi ne al’ummar Musulmi su daure su bi abin da ya inganta daga Annabi mai tsira da amincin Allah a cikin mas’alolin Aqeedah, da Ibadah, da Mu’amalah, su yi hakan shi ne wajibi a kansu, shi ne kuma alheri a gare su duniyarsu da lahirarsu. Su yi hakan shi ne wajibi a kansu koda kuwa yin hakan zai kai su ga saba wa wata magana, ko wani aiki na wani daga cikin mutanen da Al’ummah suke girmamawa; domin Annabi shi ne sama da kowa, maganarsa kuwa ita ce sama da maganar kowa.2. Tabbas yin sadlu a cikin salla sabanin sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ne, kamar yadda Malamai suka ce, misali: Sheik Abdul Aziz Bin Baaz shugaban majalisar Malamai ta kasar Saudiyya da ya gabata ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa dinsa 11/144:.Ma’ana: ((Amma sake hannaye biyu cikin salla makruhi ne, yin shi ba ya dacewa saboda kasancewarsa sabanin Sunnah; domin ya tabbata cikin Sahihiul Bukhariy daga Abu Haazim daga Sahl Bin Sa’ad Allah Ya kara masa yarda ya ce: Sun kasance ana umurtan su da cewa mutum ya dora hannunsa na dama a kan ziraa’in hagunsa cikin Sallah)).Allah Ya taimake mu har kullum.Ameen.
Dr Ibrahim Jalo Jalingo