ibnhujjah
BA A KAFA KUNGIYAR IZALAH A KAN MAZHABAR MALIKIYYAH BA:
1. Ba a kafa Kungiyar Izalah a kan mazhabar Malikiyyah ko wanin Malikiyyah ba daga cikin Mazhabobin da ke cikin fage, a'a an kafa ta ne a kan yin aiki da Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i. 2. A inda duk mazhabar Malikiyyah ko waninta suka dace da Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i, to lalle kungiyar Izalah na tare da su a nan, a inda kuma mazhabar Malikiyyah ko waninta suka saba wa Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i to lalle kungiyar Izalah ba ta tare da su a nan. 3. Lalle abin takaici ne har kullum 'yan bidi'ar da ba sa jin kunyar yi wa Duniya karya su rika cewa: an kafa kungiyar Izalah ne a kan Alkur'ani da Hadithi da kuma Mazhabar Malikiyya! 4. Tabbas babu inda lafazin ambaton mazhabar Malikiyyah ya zo koda sau daya ne a cikin constitution din Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah. Babu inda za a sami lafazin Mazhabar Malikiyyah a rubuce tun daga shafin farko na Constitution din Kungiyar har zuwa shafinsa na karshe. 5. Lalle abin da yake rubuce cikin constitution din Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah shi ne: Ita kungiya ce ta addinin Musulunci tsantsa kamar yadda Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah ya taho ta shi, wacce take dogara da Alkur'ani da Hadithan Manzon Allah da kuma Ijma'i. 6. Wannan shi ne hakikanin Kungiyar Izalah da constitution dinta, ba wai karairayin da wasu yan bidi'ah ke yadawa ba game da ita. Allah Ya taimake mu. Ameen.