ibnhujjah
BABU GURIN DA SHARI'A BA TA DA BAKIN MAGANA A CIKINSA:
1. Wasu mutane na hawan dokin jahilci suna cewa: Constitution din Nigeria ba a kan Musulunci aka gina shi ba; saboda haka kada wani ya zo da sunan Musulunci ya ce wa 'yan Nigeria ga yadda za a yi, ga kuma yadda ba za a yi ba a cikin siyasar Nigeria! Tabbas jahilcin da ke cikin irin wannan magana muninsa ya kai muni a mahangar Shari'a.
2. Gaskiyan al'amari shi ne: a dai musulunce babu wata mas'alar da ta shafi rayuwar dan adam ko aljani da babu bakin magana ga Shari'a a cikinta. Musulmi koda a gidan giya ne ya kawo kansa, ko kuwa aka kawo shi, to lalle dole ne za a samu akwai yadda Shari'ar Musulunci za ta ce ya yi a cikin wannan gidan gwargwadon yadda karfinsa zai kai; a bisa ka'idar: "Ku tsare dokokin Allah iya karfinku".
3. Ba ma a tsarin mulkin Nigeria ba da wadanda suka tsara shi sun tabbatar a cikinsa cewa akwai Allah Madaukakin Sarki, a'a koda a tsarin mulkin Kasar China ne da ba a tabbatar da cewa akwai Allah a cikinsa ba, idan har Musulmi ya sami kansa a cikin wannan Kasar a kuma karkashin wannan tsarin to dole ne lalle akwai yadda Shari'a za ta ce ya yi a bisa ka'idar: "Ku tsare dokokin Allah iya karfinku".
4. Lalle jahilai murakkabai har kullum suna kara wa kansu zunubi ne saboda irin yadda suke dogara cikin al'amuransu na yau da gobe a kan irin wannan nau'i na jahilci mai matukar muni.
Allah muke roko da Ya tausaya wa wannan Al'umma tamu Ya cusa mata fahimtar irin muni da hatsarin da yake cikin dogara da jahilci murakkabi. Ameen.