ibnhujjah
KO HANYA KADA KA YARDA YA HADAKA DA DAN BIDI’AH !!!
.
→ Yahya Dan Abi-kathir (Rahimahullah) Yace: “Idan ka hadu da ma’abocin bidi’ah a hanya, ka chanja wata hanyar.”
.
[Al’ibaana 2/475]
.
Dan bidi’ah abun zargi ne ka nisance shi domin tarayya dashi akwai hatsari matukar dai ba kira zuwa ga hanyar ALLAH kake kokarin rinjayar dashi ba, domin shi shaidan a kullum burinsa ya raba bayin ALLAH daga hanyar gaskiya zuwa ga hanyar bata, shi ko Dan adam ya kasance ma’abocin rauni saboda haka ka guji tarayya da Dan bidi’ah kada shaidan yayi nasarar rinjayarka zuwa ga bidi’ar.
.
KA KASANCE TARE DA AHLUSSUNNAH.
.
→ Imam Alwaadi’ee (Rahimahullah) Yace: ” Tafiya tare da Ahlussunnah da zama dasu da godewa ALLAH, ana la’akari dashi a matsayin maganin ciwuka da dama.”
.
[Kitaab Qam’ul mu’aanid 1/36]