ibnhujjah
Mafi yawancin jinsin halittun duniya Mazan sunfi matan kyau! Ko ka taba lura? Fahimtar wannan batu abune mai sauki, musanman in kayi dubi acikin jinsin halittun tsuntsaye da sauran matsakaitan dabbobi. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon cewa acikin ko wani jinsin samun fifiko dole ne kuma jigo ne na zaman tare, wato kafin zaman tare ya yiwu dole ne dayan yafi dayan da wani abu komai kashinsa, ballantana ma su dabbobi ba kudi garesu ba balle ma batun tinqaho na dukiya ya shigo ciki, ma'ana dai in halitta tazam iri guda babu banbanci ko fifiko to zama da mu'amulla tare bazata yiwu ba, domin duk abunda wancen yake gadara dashi kowa ma yana dashi. . Atakaice dai Acikin jinsin dabbobi kyan halitta da mazan suka fi matan da wannan kyan 'kiran ne matan suke ruduwa har suke yarje wa mazan yin mu'amulla na yau da kullum tare har kuma su hayayyafa. Kayi dubi zuwa ga ko wanne cikin dangin dabbobin da kake mu'amulla dasu yau da kullum, a nanne zaka fi fahimtar wannan batu. Yo ko meyesa acikin jinsin mutane kuma mata suke ganin kamar sunfi maza kyau? . Photunan kasa # Turaco ne mace da namiji, (mafi kyan shine namijin).