ibnhujjah
MAI AZUMIN DA YA CI ABINCI, KO YA SHA RUWA CIKIN MANTUWA YA CI GABA DA WANNAN AZUMI NASA:
1. Mai azumin da ya ci abinci, ko ya sha ruwa cikin mantuwa, ya ci gaba da azumin nasa babu kome a kansa; domin Allah Ya ciyar da shi, Ya kuma shayar da shi. Dalin wannan magana shi ne: Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 6669, da Muslim Hadithi na 1155, da Nasaa'iy Hadithi na 3262, da Ibnu Majah Hadithi na 1673, da Ahmad Hadithi na 9489, da Daaramiy Hadithi na 1767, da Ibnu Khuzaimah Hadithi na 1989, da Ibnu Hibban Hadithi na 3519, da Bazzar Hadithi na 9874 daga Sahabi Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda ya ce Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ))(( Ma'ana ))Idan dayanku ya manta cewa yana yin azumi har ya ci abinci ya sha ruwa to ya cika azumin nasa; domin ba wani abu ba ne face Allah ne Ya ciyar da shi Ya kuma shayar da shi((.
2. Dukkan shugabannin ilmin Fiqhu: Imam Abu Hanifah, da Imam Malik, da Imam Shafi'iy, da Imam Ahmad, da sauransu sun ce: Idan muka yi wata magana sannan maganar ta saba wa maganar Manzon Allah to ku bar yin aiki da maganarmu, ku yi aiki da maganar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Lalle wadannan shugabanni sun kubutar da kawunansu daga dukkan wani sharri na muqallidai.
Allah muke roko da Ya taimake mu har kullum. Ameen.