ibnhujjah
TUNANI IRIN NA KUNGIYOYIN TARZOMA ABIN MAMAKI NE MATUKA:
1. Tunani irin na kungiyoyin tarzoma a duk inda suke a kasashen duniya abin takaici ne matuka.
2. Mutane ne kuna cikin wata kasa mai rubutattun dokoki domin tsare maslaharta amma kuma ku ce ba za ku bi wadannan dokokin ba koda kuwa ba su yi karo da nassin Alkur'ani da Hadithai ba!
3. Mutane ne da a shirye suke su tsare hanya domin hana gwamnan jiha wucewa saboda kawai su nuna wa duniya cewa dokokin wannan kasa da suke cikinta su ba za su yi aiki da su ba! Mutane ne da a shirye suke su tsare hanya su hana shugaban sojojin kasar da suke cikinta wucewa saboda kawai su nuna wa duniya cewa dokokin wannan kasa da suke cikinta ba sa yin aiki da su!
4. Mutane ne da abu mafi bayyana a cikin takensu shi ne neman mutuwa a fagen gwagwarmaya da tarzoman da suka kirkira wa kansu, suka kuma lazimtar wa kansu, to amma kuma babban abin mamaki shi ne: Idan sun gamu da ajalinsu a cikin wannan tarzoma tasu sai a ga cewa sun fi kowa raki da kuka!
5. Lalle Musulunci ba ya goyon bayan hamayyar Jahiliyya, ba ya kuma goyon bayan tarzomar Jahiliyya, ba ya kuma goyon bayan taka dokokin da ba su yi karo da nassin Alkur'ani da Hadithi ba. Allah Ya kare mu daga dukkan sharri. Ameen.
Dr Ibrahim Jalo Jalingo.