ibnhujjah
YAWO BABU DAN-KWALI A TSAKAR GIDA ?
Tambaya:
Assalamu alaikum,Allah gafarta malam shin zan iya yawo acikim gida ba dan kwali?
Amsa:
Mace zata iya yawo babu Dan kwali idan tana tsakanin ‘yan uwanta mata musulmai saboda al’aurar mace ga ‘yar uwarta mace musulma tana kasancewa ne tsakanin guiwa zuwa cibiya, mutukar akwai mazan da ba muharramai ba to bai halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al’ura ce in ban da fuska da tafukan hannu. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yuauf Zarewa