Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 001 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 1
MA’ANAR DA’AWAH
.
DA’AWAH: kalma ce ta larabci wadda tushenta ya ginu akan harufan Dalun, Ainun , da Wawun da Ta’un wato Da-A-Wa-Tu () Ma’anar Kalmar a harshe shine Kira, gaiyata ko hallarowa, wato ka Kirawo ko hallaro wani zuwa gareka ko zuwa wani bigire.
.
Alal misali, Alqur’ani mai girma yayi amfani da kalmar Da’awah a wajen hallaro da matattu daga kaburbura don tsarasu filin qiyama. ALLAH (SWT) Yana cewa acikin suratul Rum:
.
.
Ma’ana: “Kuma akwai daga ayoyinsa (alamomin Kudirarsa) tsayuwar sama da Kasa bisa umurninsa, sa’annan idan Ya Kira ku, Kira d’aya daga Kasa, sai gaku kuna fita.” [Rum:25]
.
Haka kuma acikin suratul Isra’i ALLAH (SWT) Yana cewa:
.
.
Ma’ana: “A ranar da zai Kira ku sai Ku amsa da gode masa, ku dinga zaton baku zauna ba, face lokaci d’an kad’an.” [Isra’i: 52]
.
A wad’annan ayoyi da suka gabata anyi amfani da Kalmar Da’awah da Ma’anarta Kira ko halartowa.
.
● DA’AWAH a fuskar shari’ah kuma ta kunshi Kiran bayi zuwa ga addinin ALLAH, wadda ta had’a da jawo mutane zuwa ga shiga Addinin Musulunci, Tunatarwa ga Musulmi da Ilimantar dasu akan Ka’idodi da Hukunce-Hukunce da ya tattara Aqeedah, Ibadah, Mu’amala, Zamantakewa, Tarihi, Mas’alar Al’umma da duk abunda Ya shafi rayuwar Musulmi a doron kasa.
.
● DA’AWAH ta tattaro tare da game dukkan nau’o’i na shiryar da bayi da shigar da su addinin musulunci, Umurni da kyakykyawan ayyuka da hani zuwa ga mummuna. Tunatarwa (Tazkir) da Nasiha a tsakanin musulmi don zaburar dasu bisa amfani da salon bushara da gargad’i da kuma buga misalai cikin Seera da Tarihin Al’ummomi da suka gabace mu. Akwai kuma kokarin tabbatar da tsayuwa akan umurni da hani a aikace ta hanyar ayyukan Hisbah da dai sauransu.
.
● DA’AWAH Kira ne don fahimtawa ko tunatarwa ga wad’anda ake kira zuwa gare su, bisa bukatar Jan hankalin su zuwa bautar ALLAH wajen kad’aita shi a bauta, Yi masa ‘da’a, bin umurninsa, barin haninsa da rayuwa bisa tafarkinsa. Don haka aikin Da’awah ya tattara yad’a Ilimin addinin musulunci ta hanyar tunatarwa ga wad’anda suka riga suka sani, gargad’i ga masu ketare iyakan ALLAH da jawo hankalin wad’anda basu fahimci ko kar6i kiran Musulunci ba.
.
Mu had’u a FITOWA TA 2 Inshaa ALLAH.
2017-12-17 19:55 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 198 user
This Week : 198 user
This Month : 971 user
Total all : 186024 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: