Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 002 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 2
TUSHEN DA’AWAH
.
Malamai magabata sun ambata tushen da’awah cewa ya samo asali ne tun daga Annabi Adam (AS) kasancewar dukkan annabawa sun zo da alkhayri ga mutanen su, wanda kuma shine Abunda da da’awah ta qunsa.
.
Bayan shud’ewar Annabi Adam (AS) sai 6arna ta bayyana a doron qasa, don haka ALLAH (SWT) Ya turo Manzon farko don isar da saqo na kad’aita ALLAH wajen bauta.
.
An ruwaito daga Abdullahi Dan Abbas (RA) cewa akwai shud’ewar Qarnoni goma a tsakanin Annabi Adam (AS) da Annabi Nuhu (AS), wadda cikin wannan tsawon lokacin mutane suna kan tafarkin Addinin ALLAH, sai bayan shud’ewar wad’annan Qarnoni ne aka fara samun ta6ewa a tsakanin mutane, don haka ne ALLAH (SWT) ya aiko da Manzon Farko Annabi Nuhu (AS) don yin da’awah wato qiran mutanensa su dawo yiwa ALLAH ‘da’a da kad’aita shi wajen bauta.
.
A bisa wannan dalilin ne Annabi Nuhu (AS) ya kasance farkon mai da’awah, ya qira mutanensa zuwa komawa ga haqiqannin bautar ALLAH da gujewa bautar wanin ALLAH. ALLAH (SWT) Yana cewa acikin Suratul Nuhu:
.
­
.
“Lallai ne tabbas mun aiki Nuhu zuwa ga mutanensa, cewa kayi gargad’i ga mutanenka gabannin wata azaba mai rad’ad’i tazo musuYace yaku mutane na, ni agare Ku mai gargad’i ne mai bayyanawaCewa Ku bautawa ALLAH, kuji tsoronsa kuma kubi ni.” [Nuhu:1-3]
.
Daga nan Manzanni da Annabawan ALLAH wad’anda suka biyo bayan Annabi Nuhu (AS) suka d’ora, kuma wannan babban alkhayri ya kankama har zuwa ranar Aqiyama. ALLAH (SWT) Yana cewa acikin littafinsa mai girma:
.
.
” Lallai ne Mu munyi wahayi zuwa gareka, kamar yadda mukayi wahayi zuwa ga Nuhu da Annabawa daga bayansa, Kuma munyi wahayi zuwa ga Ibrahim da Isma’ila da Is’haqa da Yakubu da jikoki da Isa da Ayuba da Yunusa da Haruna da Sulaiman, kuma mun baiwa Dawuda zaburaDa wasu Manzanni, haqiqa mun bada labarinsu agareka daga gabani, da wasu manzanni wad’anda bamu bada labarinsu ba agareka, Kuma ALLAH yayi magana da Musa, magana sosaiManzanni masu bayar da bushara kuma masu gargad’i, domin kada wata hujja ta kasance ga mutane akan ALLAH bayan manzanni, kuma ALLAH Ya kasance Mabuwayi, Mai hikima.” [Nisa’i 163-165]
.
Turo da Annabawa tare da Manzon Qarshe Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), don Isar da da’awah. Ya bayyanar da cewa da’awar musulunci ita ce babbar hanyar da ake bi don farkar da al’umma daga jahilci a tsamo ta daga halaka kuma a fitar da ita daga duhun zalunci zuwa hasken imani.
.
Mu had’u a FITOWA TA 3 Inshaa ALLAH.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
2017-12-17 20:06 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 248 user
This Week : 248 user
This Month : 1021 user
Total all : 186074 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: