Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 003 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 3
Malam ya cigaba da bayani akan TUSHEN DA’AWAH da cewa:
.
Alal misali, acikin ‘yan shekaru kalilan Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi yana da’awah a garin Makkah, tun gabannin hijirarsa zuwa Madinah, wad’anda suka amsa kiransa a wannan lokaci sun samu fa’idodi masu yawa a rayuwar su. Banbanci tsakanin lokacin jahiliyya da lokacin fara da’awah ya bayyana a sarari tamkar banbanci tsakanin dare da rana.
.
Wannan al’amari ya fito fili cikin bayanin da Ja’afar Bin Abi ‘Dalib ya gabatar a lokacin da ya tashi a gaban Sarki Najjashi na Habasha, Yace: “Mun kasance mu al’umma ce dake rayuwa cikin jahiliyya, masu bautar gumaka, masu cin mushe, muna aukuwa zuwa munanan ayyuka na alfasha, muna yanke zumunta tsakaninmu, muna cutar da makwabtanmu, masu karfi daga cikin mu suna danne masu rauni. Mun kasance cikin wannan kangi har ALLAH ya aiko da Manzonsa zuwa gare mu, wanda mun san nasabarsa, Mun san gaskiyarsa da amanarsa da kamewarsa.
.
Wannan Manzo ya kira mu (wato yayi mana da’awah) zuwa ga ALLAH don mu kad’aita shi wajen bauta, mu tsarkake shi tare da kauracewa abunda mu da iyayenmu ke bautawa na daga duwatsu (gumaka), Ya umurce mu da gaskiya wajen magana da riqon amana da sada zimunci, kyautatawa maqwabt, kamewa daga ketare haddi da zubar da jini a tsakanin mu, Ya hanamu aukawa cikin ayyukan alfasha da fad’in abunda bamu da tabbas akai, da cin dukiyar maraya da yin qazafi ga salihan mata, Ya umurce mu da mu kad’aita ALLAH wajen bauta, kada mu had’a shi da kowa ……..”
.
Wad’annan kad’an kenan daga cikin kalamun babban sahabin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) a lokacin da yake bayyana irin fa’dodin da aikin da’awah na Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kawo a tsakanin al’ummah ta kuma baiwa mai rauni kariya, tana samar da tsarin rayuwa mai cike da daidaito da kyautatawa, Da’awah tana haskaka rayuwar d’an Adam ta samar masa kima da d’aukaka. ALLAH (SWT) Yana cewa:
.
.
“Ya mutanen littafi! Lallai ne, Manzon mu yaje muku yana bayyana muku abu mai yawa daga abunda kuka kasance kuna 6oyewa daga littafi, kuma yana rangwame daga abu mai yawa, Haqiqa wani haske da wani littafi mai bayyanawa yaje muku daga ALLAH ALLAH Yana shiryar da wanda yabi yardarsa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma yana fitar dasu daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma yana shiryar dasu zuwa ga hanya madaidaiciya.” [Ma’idah:15-16]
.
Mu had’u a FITOWA TA 4 Inshaa ALLAH.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA
.
2017-12-18 05:32 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 235 user
This Week : 235 user
This Month : 1008 user
Total all : 186061 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: