Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 005 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 5
NAU’O’IN DA’AWAH
.
DA’AWAH kamar yadda bayani ya gabata, kalma ce wadda ta tattaro wata hanya da za’a isar da saqon Musulunci. Don haka akwai nau’o’in isar da da’awah ga bani adam bisa la’akari da irin mutanen da ake yiwa da’awar daga yanayin rayuwarsu da kuma salo ko yanayin isar musu da saqon.
.
Wato ana gabatar da da’awah ne bisa nau’in da ya dace da saqon da ake qoqarin isarwa ga al’umma, A bisa wannan ne aka umurci Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya gabatar da aikin da’awah bisa nau’o’i ko salon-hikima, ta hanyar wa’azi mai kyau da kuma jayayya bisa Abunda yake mafi kyau a tsakanin wad’anda yake isarwa saqon.
.
Ana la’akari da irin saqon da ake isarwa da kuma wadanda ake buqatar isarwa zuwa gare su wajen amfani da wani nau’i na da’awah, wasu daga cikin nau’o’in da’awah sun had’a da IRSHAD ko shiryarwa zuwa ga addinin musulunci, Umurni da kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munanan da dai sauransu.
.
SHIRYARWA ZUWA GA ADDININ MUSULUNCI (IRSHAD KO DA’AWAH)
.
Wannan aikin da’awah ne wadda ya qunshi isar da saqon musulunci ga al’ummomi ko mutanen da basu kar6e shi ba, daga cikin masu riqe da littafi ko kuma masu bautar wanin ALLAH da kuma wad’anda basu da wani addini baki d’aya, wannan shine jigon abunda aka aiko dukkan Annabawa da Mursalai akai. Wato qiran mutane su kad’aita ALLAH wajen bauta ta hanyar barin addinin qarya da suke bi, ko kuma domin su fahimci muhimmancin rayuwa cikin addini, ga wad’anda basu yi riqo ga ko wani addini ba kuwa sai ya zamanto hanyar jan hankalinsu zuwa ga addinin Musulunci.
.
A qarqashin wannan Nau’u na da’awah, tilas ayi la’akari da irin mutumin da za’a isar wa wannan saqo, Alal misali ya kamata a fahimci wane tafarki yake akai, menene fahimtarsa ga rayuwa da addini, ya iliminsa da wayewarsa yake da dai sauransu.
.
Malam Ahmad Deedat (ALLAH Yayi masa Rahama), malami ne da ya shahara wajen qiran mabiya addinin kirista zuwa ga musulunci, ya bada wani misali na yadda ake la’akari da yanayin irin mutumin da ake yiwa da’awah ayayin isar da saqon ALLAH, yayi nuni da yadda ALLAH (SWT) da kansa ya amsawa wasu rukunnan al’umma guda biyu a lokacin da suke da’awar jingina shi da ‘Ya’yaye ko suka yi masa tarayya awajen kad’aitakarsa.
.
Mu had’u a FITOWA TA 6 Inshaa ALLAH.
2017-12-18 05:42 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 161 user
This Week : 161 user
This Month : 934 user
Total all : 185987 visitors
LAST PAGES

Teya Salat



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: