pacman, rainbows, and roller s

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 009 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 9
Malam ya cigaba da bayani akan UMURNI DA KYAWAWAN AYYUKA DA HANI ZUWA GA MUNANA.
.
Game da d’aid’aikun jama’a ALLAH (SWT) Ya siffanta muminai maza da mata da kasancewa masu aikin Umurni da kyawawan ayyuka da hani ga munana acikin littafinsa Maigirma inda Yake cewa:
.
.
“Kuma muminai maza da muminai mata sashensu maji6incin sashe ne, suna umurni da alkhayri kuma suna hani da abunda ba a so, kuma suna tsayar da Sallah, kuma suna bayar da zakka, kuma suna d’a-a ga ALLAH da Manzonsa, wad’annan ALLAH zai yi musu rahama, Lallai ALLAH shine Mabuwayi Mai hikima.” [Taubah:71]
.
Haka kuma hadisan Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) sun qarfafa wannan muhimmin aiki a tsakanin al’ummomin musulmai, Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Duk wanda yaga wani abun Qi ya chanja shi da hannunsa, idan bazai iya ba ya chanja shi da harshensa, idan bazai iya ba yaqi shi a zuciyarsa wannan shine mafi raunin imani.” [Imam Muslim]
.
Har ila yau acikin wani hadisi ruwayar Ahmad, Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Na rantse da wanda rai na ke hannunsa ko kuyi Umurni da kyawawan aiki, kuma kuma kuyi hani da munanan aiki ko kuma ya yi kusa ALLAH ya aiko muku da bala’i kuma idan kuka roqe shi bazai amsa muku ba.” [Imam Ahmad]
.
A qarqashin wannan nau’i na da’awah ana iya samun salo daban-daban na tunatarwa, Ana iya amfani da salon bushara (Jan hankali zuwa ga tanadin nau’o’in ni’ima da aka Samar don sakamako ga masu d’a-a da bin ALLAH), Gargad’i (na irin tanadin narkon azaba ga masu qetare iyakokin ALLAH), Bada labarun abubuwa da suka gabata na daga al’ummomin Annabawa da Alqur’ani ya ambatana da kuma rayuwar Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sahabbansa da dai sauransu.
.
Mu had’u a FITOWA TA 10 Inshaa ALLAH.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
2017-12-18 06:29 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 164 user
This Week : 164 user
This Month : 937 user
Total all : 185990 visitors
LAST PAGES



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: