pacman, rainbows, and roller s

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 012 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 12
.
Malam Ya cigaba da bayani game da DA’AWAH TA HANYAR AIKIN HISBAH
.
Haqiqa ayyukan da’awah a qarqashin Hisbah ya tattara abubuwa masu yawa wadda ya shiga cikin aqidah, ibadah, Mu’amala da zamantakewar al’ummar musulmai, sannan kuma aikin Hisbah ya samo asali ne daga ayyukan Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da khalifofinsa masu daraja. Misalin irin ayyukan Hisbah na Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) sune:
.
1● An kar6o hadith daga Abdullahi Bin Abbas (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya goya Fadhl Ibn Abbas a bayan taguwarsa, sai ga wata mace daga qabilar khash’an tazo (don fatawa), sai Fadhl Bin Abbas ya juya yana kallonta itama tana kallonsa, sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yasa hannunsa ya kautar da fuskar Fadhl zuwa 6angare daban.” [Imamul Bukhari]
.
2● An kar6o hadith daga Abu-hurayrah (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya wuce ta wajen wani sanhon abinci, sai yasa hannunsa aciki sai yaji danshi-danshi, sai Yace: Menene Wannan kai mai sayarda abinci? Sai yace ruwan sama ne ya doke shi, sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Menene yasa baku sanya jiqaqqun a sama ba, don mutane su gani? Duk wanda ya mana algus (Ha’inci) baya tare da mu.” [Imam Muslim]
.
3● Ankar6o daga Abdullahi ‘Dan Umar (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya umurceni da inzo masa da wuqa mai kaifi, sai naje na kawo masa ita, sai ya aika aka waso masa ita, sannan sai yace gobe kazo mini da ita, sai nazo da ita washegari. Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yaje kasuwar Madina tare da sahabban sa. Acikin kasuwar kuma akwai sulkunan giya wad’anda aka kawo daga Sham, sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kar6i wuqar nan daga hannu na, ya huhhuda wad’annan salqunan giyar, sannan ya bani wuqar ya umurci sahabban sa wad’anda suke tare dashi da su wuce gaba su taimaka mini. Ni kuma Yace da ni ka zaga kasuwannin gaba d’aya kada ka bar wata salqar giya face ka huda ta. Haka kuwa na aikata, banbar salqar giya ba acikin kasuwannin nan face na huda ta.” [Musnad Imam Ahmad]
.
Irin wad’annan ayyuka na da’awah sun gudana a lokacin khalifofin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kuma wad’anda suka biyo bayansu da kyautatawa. Kuma yana daga cikin ayyukan alkhayri masu fa’idah da ake buqatar masu jagorancin al’ummar musulmai suyi kwad’ayin tabbatarwa acikin mulkinsu domin samun tsira aranar qarshe.
.
Amma aikin bai taqaita ga shuwagabannin al’umma kawai ba, a’a aiki ne da ya kamata ya gudana a tsakanin musulmai. Wallahu A’alam.
.
Mu had’u a FITOWA TA 13 Inshaa ALLAH.
^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
2017-12-31 00:00 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 130 user
This Week : 130 user
This Month : 903 user
Total all : 185956 visitorsUnited States
LAST PAGES



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: