Ring ring

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 016 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 16
.
Malam ya cigaba da bayani game da HUKUNCIN DA’AWAH.
.
2● DA’AWAH A MATSAYIN FARDUL KIFAYAH:
.
Mafi yawan malamai sun raja’a akan cewa da’awah aiki ne na fardul kifayah wato aiki ne da ya wajaba akan dukkan musulmai, amma idan wasu yanki na jama’a zuka rungumi gabatar da wannan aiki, wajibcin yin aikin ya sauka akan sauran jama’a.
.
Wannan ra’ayi ya ginu ne bisa hujjar cewa: ALLAH (SWT) acikin ayar da yayi umurnin aikin da’awah, cikin suratul suratul Ali-imran cewa yayi: “Kuma wata jama’a daga cikinku ta kasance…” wato yankin jama’a ba kowa da kowa ba.
.
Ibnul Arabi yana da ra’ayin cewa fadin ALLAH cewa: “Za’a samu wasu al’umma daga cikinku” wanda ishara ne da wajibcin yin da’awah, yana nuni ne da kasancewar da’awah Fardul kifayah ne.
.
Haka ma Imam Ibnu Kathir acikin tafsirin wannan aya ya bayyana cewa: wannan aya tana nusar da cewa dole a samu wani rukuni daga cikin al’ummar musulmai da zasu rungumi aikin umurni da kyawawan aiki da hani zuwa ga munana, duk kuwa da kasancewa wannan aiki yana kan ko wani musulmi gwargodon iyawarsa.
.
Sheikh ibn Taimiyyah ya jaddada wannan ra’ayi, inda yake cewa: “umurni da kyawawan ayyuka da hani da munana bai wajaba akan kowa da kowa bisa kasancewarsa Fardul Ain ba, sai dai bisa kasancewarsa Fardul kifayah, wato wasu mutane zasu iya daukewa wa wasu, kamar yadda dalilai suka tabbata acikin alkur’ani…” Amma idan aka rasa samun wadanda zasu gabatar da wannan muhimmin aiki, wato aka bar aikin da’awah baki daya, to anan ukubar da zata biyo baya zata game kowa da kowa, kuma a wannan lokaci yin da’awah ya hau kan dukkan musulmai baki daya babu wanda zai fita.
Mu had’u a FITOWA TA 17 Inshaa ALLAH.
2018-01-31 02:02 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 137 user
This Week : 137 user
This Month : 910 user
Total all : 185963 visitorsUnited States
LAST PAGES



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: