XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah ANNABI YA RUBUTA WA JARIRIYAR DAULAR ISLAMA A MADINA CONSTITUTIONAbu ne mai wahalar gaske a samu wata gamayya ta al’umma ko wata hadaka ta jama’a wacce za a ce ba a tsara wa gudanar da ita constitution ba: ko dai a rubuce, ko kuwa ba a rubuce ba.Wannan shi ya sa ma a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi hijira zuwa Madina bai bata wani lokaci ba, a’a tun a shekarar farko ta hijira ne ya rubuta wa jaririyar Daular Islama constitution: watau abin da tsoffin littattafan tarihi na Musulunci ke kira:AL-WATHIIQAH ma’ana: Abin da aka kyautata shi kuma aka amince da shi. Wani lokaci kuma suna kiran shi da suna: AS-SAHIIFAH ma’ana:Littafi. Sannan sabbin littattafan tarihin Musulunci kuma suna kiran shi da suna:DUSTUURUL MADINAH ma’ana constitution din Madina.Ga tarjamar nassin constitution din kamar yadda ya zo a rubuce cikin littafin: Siiratu Ibn Hisham 1/503, da littafin Ar-Raudhul Unuf 2/345, da littafin As-Siiratun Nabawiyyah Ardhu Waqaa’i’i Wa Tahliilu Ahdath 1/492:-((Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.Wannan wani littafi ne daga Muhammad Annabin nan kuma Manzon Allah, tsakanin Muminai da Musulmai daga Quraishawa da mutanen Yathrib (Madina) da ma wanda ya bi su ya riske su ya yi jihadi tare da su.Lalle su wata Al’umma ce guda daya koma bayan mutane.Muhaajirai daga cikinsu Quraishawa za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai: za su rika biyan diyya a tsakaninsu, za su rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinsu a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Banuu Auf za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai: Za su rika biyan diyya a bisa diyyarsu ta farko, ko wace jama’a za ta rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinta a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Banul Haarith Bin Khazraj za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai: Za su rika biyan diyya a bisa diyyoyinsu na farko, ko wace jama’a za ta rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinta a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Banuu Jusham za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai: Za su rika biyan diyya a bisa diyyoyinsu na farko, ko wace jama’a za ta rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinta a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Banun Najjar za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai: Za su rika biyan diyya a bisa diyyoyinsu na farko, ko wace jama’a za su rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinta a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Banuu Amr Bin Auf za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai: Za su rika biyan diyya a bisa diyyoyinsu na farko, ko wace jama’a za ta rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinta a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Banun Nabit za su ci gaba da zama a kan al’amarin da suke a kai za su rika biyan diyya a bisa diyyoyinsu na farko, ko wace jsma’a za ta rika fansar fursunonin yaki da aka kama daga cikinta a bisa tsari na kyautayi da adalci a tsakanin Muminai.Lalle Muminai ba za su bar mutumin da bashi ya ci karfinsa a cikinsu ba face sai sun ba shi abin da zai biya tare da kyautayi: Daga fansa ko diyya.Sannan Mumini ba zai yi kawance da ‘yantaccen bawa na wani Mumini ba koma bayan wancan Muminin.Kuma lalle Muminai masu takawa hannuwansu yana kan dukkan wanda ya yi zalunci a cikinsu ko ya nemi samun wata kariya ta hanyar zalunci, ko zunubi, ko ketare iyaka, ko yada barna tsakanin Muminai, lalle hannuwansu suna kansa gaba daya koda kuwa da ne yake ga daya daga cikinsu.Sannan Mumini ba ya kashe Mumini saboda kafiri, haka nan ba zai taimaki kafiri a kan Mumini ba.Kuma amanar Allah daya ce mafi kankanta a cikin Muminai in ya dauke ta hakan sai ya lazimce su (gaba daya).Kuma lalle Muminai sashinsu majibinci ne ga sashi koma bayan sauran mutane.Kuma lalle dukkan wanda ya bi mu daga cikin Yahudawa to yana da hakkin taimako da koyi a bisa halin suna wadanda ba a zalunta, kuma ba a taimakon wani a kan cutar da su.Kuma lalle zaman lafiyar Muminai daya ce ba za a kulla zaman lafiya da wani Mumini ba koma bayan wani Muminin a cikin yaki cikin tafarkin Allah face sai a bisa daidai da adalci a tsakaninsu.Kuma lalle ko wane yaki da ake aiwatarwa za a rika karbabbeniya ne a tsakaninsu (idan wadannan jama’a suka fita a wannan yakin to wasu jama’an kuma sai su fita a daya yakin).Kuma lalle Muminai sashinsu na dawowa a kan sashi da abin da ya sami jininsu cikin tafarkin Allah.Kuma lalle Muminai masu takawa suna bisa mafi kyawun shiriya kuma mafi mikewansa.Sannan wani mushruki (mai bautar gumaka) ba zai ba da mafaka ga wani rai ko dukiya ta Quraishawa ba, kuma ba zai shiga tsakanin wani Mumini da shi ba (shi wannan ran ko dukiyar).Sannan duk wanda ya yi kisan kai a bisa zalunci kisa kuma wanda ya tabbata ta hanyar hujja to za a yi kisasi ne (ramuwar gayya) a cikinsa sai dai idan waliyyin wanda aka kashe ya yarda ya karbi diyya, sannan dole ne dukkan Muminai su tsayu a
2018-03-14 14:24 · Reply · (0)
* ibnhujjah * ibnhujjah kansu babu abin da zai halatta gare su sai tsayuwa a kansa.Sannan ba ya halatta ga Muminin da ya yarda da abin da ke cikin wannan Littafin (constitution) kuma ya yi imani da Allah da Ranar Lahira ya taimaki mai laifi, ko ya ba shi mafaka kuma lalle duk wanda ya taimake shi ko ya ba shi mafaka to hakika akwai la’anar Allah a kansa, da kuma fushinSa a Ranar Kiyama, sannan ba za a karbi wata musanya ko fansa daga gare shi ba.Sannan duk yadda kuka saba a cikin al’amari to fa makomarsa zuwa ga Muhammad mai tsira da amincin Allah ne.Lalle Yahudawa za su rika ciyar da dukiyarsu tare da Muminai matukar dai ana yakarsu (su Muminan).Sannan Yahudawa Banuu Auf wata Al’umma ce tare da Muminai.Yahudawa suna damar yin addininsu, Musulmi ma suna da daar yin addininsu: ‘Yantattun bayinsu da su kansu sai wanda ya yi zalunci ya yi zunubi, lalle shi wannan babu wanda yake hallakarwa sai kansa da kuma iyalan gidansa.Kuma lalle Yahudawan Banuu Najjar suna da keatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf suke da shi.Sannan Yahudawan Banul Haarith suna da kwatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf auke da ahi.Sannan Yahudawan Banuu Saa’idah suna da kwatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf suke da shi.Sannan Yahudawan Banuu Ju’sham suna da kwatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf suke da shi.Sannan Yahudawan Banul Aus suna da kwatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf suke da shi.Sannan Yahudawan Banuu Tha’ala’bah suna da kwatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf suke da shi.Sai fa wanda ya yi zalunci ya yi zunubi lalle shi wannan babu wanda yake hallakarwa sai kansa da kuma iyalan gidansa.Kuma lalle jama’ar Jafnah wani yanki ne na Kabilar Tha’ala’bah saboda su kamar su suke.Kuma lalle Banuu Sha’tai’bah suna da kwatankwacin abin da Yahudawan Banuu Auf suke da shi.Sannan aikin kirki ba kamar zunubi yake ba.Sannan ‘yantattun bayin Tha’ala’bah kamar su Tha’ala’bah ne suke.Sannan abokan Yahudawa kamar su kansu Yahudawan ne suke.Sannan babu daya daga cikinsu da zai fita ba tare da izinin Muhammad mai tsira da amincin Allah ba.Sannan ba za a sanya kariya ba a kan daukan fansar wani rauni.Sannan duk wanda ya yi kisan gilla to kuwa kansa da iyalansa ya yi wa’ sai fa wanda ya yi zalunci, kuma lalle Allah Yana kan magi kyawun haka.Sannan wajibi ne Yahudawa su ciyar da dukiyoyinsu, kuma wajibi ne Musulmi su ciyar da dukiyoyinsu.Sannan lalle akwai taimakon juna a tsakaninsu a kan dukkan wanda ya yaki mutanen wannan Littafin (constitution).Sannan lalle a tsakaninsu akwai nasiha da ayyukan kwarai banda zunubi.Sannan ba a cewa mutum ya yi laifi saboda dalilin abokin kwancensa.Sannan lalle akwai taimako ga wanda aka zalunta.Sannan kuma Yahudawa za su ciyar da dukiyoyinsu tare da Muminai matukar dai ana yakarsu.Sannan garin Yathrib (Madina) lalle mai alfarma ne ga mutanen wannan Littafin (Constitution).Sannan lalle makwabci tamkar makwabcinsa yake matukar ba mai cutarwa ba ne ba kuma mai zunubi ba ne.Sannan ba a ba wa wata mace mafaka ba tare da izinin mutanenta ba.Sannan dukkan abin da ya kasance a tsakanin jama’ar wannan Littafin (constitution) na wani laifi ko wani jayayya da ake tsoron barnarsa, to makomarsa zuwa ga Allah ne kuma zuwa ga Muhammad Manzon Allah ne mai tsira da amincin Allah.Sannan Allah Yana a kan mafi kirki da takawar abin da yake cikin wannan Littafin (constitution).Sannan ba a bai wa Quraishawa da wadanda suka taimake su mafaka.Sannan lalle taimako dole ne a tsakaninsu a kan dukkan wanda ya kawo wa Yathrib (Madina) hari.Idan kuma aka kira su zuwa ga wani sulhu da za su yi shi kuma su jibance shi to lalle za su yi sulhun kuma za su jibance shi, lalle su idan aka kira su zuwa ga misalin haka to lalle ne suna hakki a kan Muminai face wannan da ya yi yaki cikin Addini.A kan dukkan mutane akwai kaso nasu ta bangarensun nan da yake ta fiskarsu.Kuma lalle Yahudawan Aus: ‘Yantattun bayinsu da su kansu suna kan misalin abin da ma’abuta wannan Littafin (constitution) suke da shi tare da tsantsar mutumin kirki daga ma’abuta wannan Littafin (constitution).Kuma lalle aikin kirki ba kamar zunubi yake ba, babu wani mai aikata wani aiki na barna face a kan kansa.Kuma lalle Allah Yana kan mafi gaskiya kuma mafi kirkin abin da yake cikin wannan Littafi (constitution).Kuma lalle wannan Littafin (constitution) ba ya ba wa azzalumi da mai zunubi kariya.Kuma lalle dukkan wanda ya fita daga Madina amintacce ne, kuma dukkan wanda ya zauna cikin Madina amintacce ne, sai wanda ya yi zalunci, ko ya yi zunubi.Kuma lalle Allah Mai ba da mafaka ne ga wanda ya yi kirki da takawa, haka ma Muhammad Manzon Allah mai tsira da amincin Allah)). Intaha.*************************wannan ita ce:-– – Da Annabi mai tsira da amincin Allah ya rubuta wa mutanen Madina Musulminsu da Yahudawansu da kafurai masu bautan gumaka dake tare da su.Kuma Annabi ya rubuta musu wannan constitution din ne ba saboda da yaudara ba a’a saboda su yi aiki da shi ne.Ke nan wannan yana tabbatar mana da cewa duk lokacin da Musulmi masana Shari’ar Musulunci suka hadu suka rubuta constitution saboda gudanar da kasar
2018-03-14 14:31 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 222 user
This Week : 222 user
This Month : 995 user
Total all : 186048 visitorsUnited States
LAST PAGES



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: