Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 1. Ba dukkan hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah ba ne Babban Malamin Hadithi da Fiqhu Imam Malik ya sani ba, a’a ya dai san mafi yawansu amma kuma bai san dukkansu ba, wannan kuma ita ce siffar dukkan wani malami cikin wannan Al’ummah tun daga zamanin Sahabbai har zuwa karshen Duniya.
2. Lalle a cikin hanyoyin da ‘yan bidi’ah ke bi domin neman raba mutane da bin sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah a cikin mas’alolin Aqeedah, da Ibadah, da Mu’amalah akwai nuna musu cewa: Wannan hadithin Sahabi wane bai yi aiki da shi ba, ko Taabi’iy wane bai yi aiki da shi ba, ko Taabi’ut Taabi’iy wane bai yi aiki da shi ba, ko Imam Abu Hanifah bai yi aiki da shi ba, ko Imam Malik bai yi aiki da shi ba, ko Imamush Shaafi’iy bai yi aiki da shi ba, ko Imam Ahmad bai yi aiki da shi ba, ko Waliyyi Shehu wane bai yi aiki da shi ba, ko uban tafiya Malam wane bai yi aiki da shi ba; saboda haka lalle da yin aiki da shi wannan hadithin ya halatta to da kuwa ba a sami wani daga cikin irin wadannan manyan mutane da zai yi watsi da shi ya kuma ki yin aiki da shi ba!!
3. A nan ga shaidar cewa: a cikin almajiran Imam Malik ma akwai wanda ya san hadithin da shi Imam Malik bai sani ba, kuma wannan ba nakasa ba ce ga shi Imam Malik, a’a abu ne da ke kara fito da irin mutuntakarsa:-
Baihaqiy ya ruwaito hadithi na 364 daga Ahmad Bin Abdirrahman Bin Wahb ya ce:-
((: : . : . : : : : . : . )).
Ma’ana: ((Na ji baffana yana cewa: na ji Malik ana tambayar shi game da tsettsefe yatsun kafa cikin alwala, sai ya ce: ba wajibi ba ne a kan mutane.
Sai na bar shi har mutane suka ragu, sannan na ce: Abu Abdillah, na ji ka kana ba da fatawa game da wata mas’alah, game da tsefe yatsun kafa, ka riya cewa hakan ba wajibi ba ne a kan mutane, lalle mu muna da sunnah. Sai ya ce: wace ce? Sai na ce:
Laith Bin Sa’ad, da Ibnu Luhai’ah, da Amr Bin Haarith sun gaya mana daga Yazid Bin Amr Al-Ma’aafiriy, daga Abu Abdurrahman Al-Hubuliy, daga Mustaurid Bin Shaddad Al-Qurashiy ya ce: Na ga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana goge tsakanin yatsun kafarsa da karamar yatsarsa”.
Sai ya ce: Lalle wannan hadithi mai kyau ne, amma ban taba jin shi ba sai wannan lokacin. Daga bayan wannan sai na ji ana tambayar shi kuma yana ba da umurni da goge yatsu)).
4. Ga shi dai karara wannan mas’ala ce muhimmiya daga cikin mas’alolin da suka shafi alwala kuma wacce Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi umurni da ita cikin ingantaccen hadithi amma kuma ga shi Imam Malik bai san hadithin ba, wannan ma shi ne ya sa ya yi fatawa da sabanin abin da Annabi ya yi umurni da shi, to amma alhamdu lillahi almajirinsa Abdullahi Bin Whab ya koyi hadithin daga waninsa, da kuma ya gaya masa nan da nan ya bar ra’ayinsa da ijtihadinsa ya koma a kan abin da Annabi ya yi umurni da shi. Madalla da wannan hali na Imam Malik, saboda wannan abin da ya yin shi ne dukkan ahlussunnah na gaskiya ke yi, babu wadanda ke taka ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah su bi ra’ayoyinsu ko ra’ayoyin malamansu sai ‘yan bidi’ah wadanda ba sa ganin kimar hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.
2018-03-08 08:44 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 120 user
This Week : 120 user
This Month : 893 user
Total all : 185946 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: