Insane

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAMAMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-... Readmore..
post An Rubuta Ranar 23/07/18
AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAMAMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM. ... Readmore..
post An Rubuta Ranar 22/07/18
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam... Readmore..
1234...555657»

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah JAKKAR MAGORIN MUSULUNCI, WALLAFAR (MALAM SANI LIMAN TSAFE) LIMAMIN MASALLACIN JUMA’A NA ABU HURAIRA AREA II TSAFE.
*MENENE BANBANCI TSAKANIN MALAMI DA BOKA*
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) wanda yake shiryadda wanda yaso akan tafarki madaidaici. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (S.A.W.) wanda ya bayyana mana hanyoyin kusanta zuwa ga Allah (S.W.T).
Bayan haka, wajibi ne a jawo hankalin yanuwa domin su gane bambamci tsakanin malami na gaskiya da wanda a zahiri yake sa rigar malanta, amma a boye shi boka ne.
Akwai alamomi da yawa da suke nuna cewa mutum boka ne koda kuwa a zahiri yana nuna shi malami ne. Daga cikin wadannan alamomi akwai:-
Wanda idan akaje wajensa neman taimako sai ya tambayi sunan wanda yazo da sunan mahaifiyarsa da mahaifi.
Wanda yake cewa mai neman taimako ya kawo wani abu nashi a hada ayi aiki. Misali takalmi ko riga ko gashi ko akaifa da sauransu.
Wanda a wasu lokutta da ka shiga wajensa zai fadi sunanka da inda ka fito da sauransu, alhali kai baka taba saninsa ba.
Wanda yake cewa a kawo wasu abubuwa da babu su ko kuma masu wuyar samu, kamar bera maraya, ko beraye goma sha daya wanda aka kama suna barci ko biri makaho da dai sauransu. Idan baka iya kawosu sai yace ka bada kudi a samu mai kawosu.
Wanda yake karance karancen shirme da kiran wanin Allah kamar Aljannu da shedanu da waliyyai da sauransu.
Wanda zaice a kawo wasu nauoin dabbobi kamarsu bakar akuya wadanda zaayi aiki da su, ko a umurci maras lafiya yaje ya binne irin wadannan dabbobi gindin wani itace ko dutse.
Wanda yake wulakanta kurani ta hanyar rubuta shi da najasa kamar jinin biki ko na haila.
Wanda yake bugun kasa domin ya gayawa mutum abinda zai samu ko ya same shi anan gaba.
Wanda yake ba mai bukata ko maras lafiya wani abu kamar kaho ko kambu ko laya, koma dai duk wani abu wanda a cikinsa adduoi ne na shirme da shirka, a umrceshi ya rataya ko ya aje karkashin matashi.
Wanda yake zana siffofin aljannu (dalamusai) a takarda ya jika takardar a ruwa kuma ya umurci maras lafiya yayi wanka da ruwan a wani wurin da baa ganinsa kamar makabarta ko wani kangon gini.
Wanda yake umurtar mai bukata yasa rigar layu ko Falmara wadda aka zana mata dalamusai ko wasu lambobi
Wanda yake bada wani abu da manufar zai iya sa mace taso miji ko kuma mallakeshi da dai wani abu mai kama da wannan.
Wanda yake umurnin direba ya daura kan kura ko hakorinta ko wani kyalle ga motar da manufar wai wannan zai kareshi daga hadari.
Wanda yake umurnin masu mota su lika charbi ko hoton wani Shehi a gilas din motar da manufar wannan charbi ko Shehi zai kare wannan mota daga hadari.
Wanda yake umurtar a lika hoton Shehi ko layu a gida ko ofis ko shago da manufar wadannan abubuwan zasu iya jawo wani alheri ko kare wani sharri.
Wanda yake amfani da kwai wanda aka zana dalamusai ko kuma kwado na rufe kofa da riyawar cewa wannan yana iya rufe bakin wani.
Wanda zai bada wasu abubuwa yace aje a rufe wasu kebantattun wurare, kamarsu gulbi ko makabarta ko suri ko magamar hanyoyi da sauransu.
Wanda yake bada wani irin zobe, yawanci na azurfa wanda aka zanawa dalamusai da manufar wannan zobe zai iya jawo mashi wani alheri ko ya kauda mashi wani sharri.
Wanda yake amfani da allon karfe ko tafasashshiyar dalma domin wai kona wani da ake son a halaka.
Wanda ke bada labari ga maras lafiya cewa wani ne ya jefe shi ko kuma yayi masa wani kafi a gidansa.
Wanda wasu alamonin fasikanci suka bayyana gareshi. Misali wanda ke aske gemu, ko ya bar gashin baki bazo-bazo, ko sakin wando ko riga suna jan kasa ko kuma rashin halartar sallar jami.
Wanda yake duba na charbi. Wato yana amfani da charbi ta yin zane dashi ko kuma ba mabukaci charbin yana ja da riya cewa idan yakai wuri kaza na charbin to akwai alheri, amma in ya tsaya wuri kaza na charbin to wannan sharri ne.
FADAKARWA
Wadannan alamomi da aka ambata kadan ne daga cikin hanyoyin da ake bi wajen zare imanin mutum da halakar dashi da sunan malanta. Don haka wajibi ne mutum yayi hankali da Yan-duba da bokaye da malamam tsibbu. Manzon Allah (S.A.W.) yace Wanda yaje wajen boka ko malamin duba, kuma ya gasagata abinda suka fada to ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi (S.A.W.) . A wata ruwayar Manzon Allah (S.A.W.) yace :Wanda yaje wajen Boka ko Dan Duba amma bai gasgata abinda suka ce ba, baida sallar kwana 40. Malamai 4 suka ruwaito wannan Hadisi.
ALLAH YA TSARE MANA IMANINMU AMIN.
2018-02-23 07:57 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 146 user
This Week : 146 user
This Month : 919 user
Total all : 185972 visitorsUnited States
LAST PAGES



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: