ibnhujjah
013 DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH
FITOWA TA 13
.
FALALAR DA’AWAH
.
Da’awah tana da fa’ida da falala mai yawa, ta dukkan fuskoki, Da’awah tana da dunbun falala ta fuskar wadanda ake isarwa sakon da kuma ta bangaren masu aikin isar da sakon. ALLAH (SWT) Yana cewa acikin littafinsa Maigirma:
.
.
“Kuma wanene Mafi kyau ga magana daga wanda yayi kira zuwa ga ALLAH, kuma ya aikata aiki na kwarai, kuma yace, ‘lallai ni, ina daga masu sallamawar al’amari zuwa ga ALLAH (musulmai).” [Fussilat:33]
.
Daga wannan zamu iya fahimtar irin tarin alherin dake cikin aiki da’awah da ladan da ALLAH ya tanada saboda masu wannan aiki. Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yayi bayanin falala mai yawa da mai aikin da’awah yake dashi. Wasu daga cikin hadisan da suke nuni zuwa ga falalan masu da’awah sun hada da hadisin:
.
● Abu-hurairah (RA) cewa: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Duk wanda yayi kira zuwa shiriya, yana da lada tamkar Ladan wanda yayi aiki da wannan shiriyar, ba tare da an rage ladar wanda yayi aikin da shiryarwar ba, haka kuma wanda yayi kira zuwa ga bata yana da zunubin wanda yayi aiki da kiransa, ba tare da an rage zunubin wanda ya aikata wannan mummunan aikin (Batan) ba.” [Imam Muslim]
.
● Haka Kuma, Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Mutum daya ya samu shiriya ta hannunka yafi da a baka jajayen rakuma.” [Bukhari da Muslim]
.
● A wani hadisin kuwa, Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Duk wanda ya shiryar zuwa wani alheri, yana da (Sakamako) daidai da wanda ya aikata wannan aiki.” [Imam Muslim]
.
Mu had’u a FITOWA TA 14 Inshaa ALLAH.
.