ibnhujjah
NAFILA BAYAN SALLAR ASUBA!!
Tambaya:Assalamun alaikum
Barka da wannan lokaci barka da tashi , malam dan Allah tambaya ce dani , malam dan Allah , anayin nafillah bayan sallah asubahi , ya in ganta daga manzon Allah . Nagode
Amsaa:
Wa alaikum assalam, To dan ‘uwa Annabi s.a.w. ya haramta yin sallah bayan sallar asuba har sai rana ta fito, amma wanda raka’atanil Fajr ta wuce shi kafin asuba, zai iya ramawa , bayan sallar asuba, saboda Annabi S.a.w ya ga wani yana ramawa bai yi masa inkari, ba, hakan sai ya nuna halaccinsa, Kamar yadda ya inganta a wajan Abu-dawud a hadisi mai lamba ta: 1267
Allah ne mafi sani
Jamilu ZAREWA