Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS

BA'ABARIN INGAN TACCEN HADISI SABODA YA SABAWA MAZAHABA

BA A BARIN INGANTACCEN
HADITHI SABODA YA SABA WA
WATA NAZHABA:
2. Matafiyar Annabi mai tsira da
amincin Allah ita ce sama da
dukkan wata matafiya (mazhaba),
sannan fiqhunsa shi ne sama da
dukkan wani fiqhu.
2. Bin mazhabar (matafiyar) wani
malami daga cikin Malaman
Musulunci ba laifi ba ne matukar
dai hakan bai kai mutum ga barin
yin aiki da wani ingantaccen
hadithin manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ba, in kuma ya kai shi
ga barin yin aiki da wani
ingantaccen nassin hadithin Annabi
to lalle hakan ya haramta a bisa
ittifakin dukkan Magabata na
kwarai; saboda Annabi
Muhammadu ne kawai Allah Ya
aiko wa wannan Al’umma, duk
kuma wani wanda ba shi ba to
mabiyi yake a gare shi, kuma
maganarsa shi Annabi Muhammadu
tana sama da maganarsa.
3. To amma in aka sami wata
mas’ala da babu nassin Annabi mai
tsira da amincin Allah a kanta to a
nan dukkan wani malami mai ikon
yin ijtihadi sai ya yi ijtihadinsa kuma
duk hukuncin da ya samu kaiwa
gare shi cikin ijtihadin nasa to da
shi ne zai bauta wa Allah
Ubangijinsa. Sannan kuma shi
aammiy mara ikon yin ijtihadin Ilmi
sai ya yi koyi da wanda zuciyarsa ta
fi kwanciya da shi cikin mujtahidan
da suka yi ijtihadin Ilmi a cikin
wannan mas’ala wacce babu
ingantaccen nassin Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah a cikinta.
4. Ke nan wajibi ne a kan ko wane
musulmi ya gina addininsa a kan
sunnar Annabi mai tsira da amincin
Allah; saboda duk wanda ya bar yin
aiki da ingantaccen hadithin Annabi
mai tsira da amincin Allah cikin
wata mas’ala daga cikin mas’aloli
kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a
bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta
saba wa hadithin, ko wata darika
tasa ta Sufaye ta saba wa hadithin,
ko wani tsari na kungiyarsa ya saba
wa hadithin, ko wani tsari na
duniyarsa ya saba wa hadithin to
lalle wannan ya bace ya bar hanyar
Muminai, ya bar fikhun Sahabbai da
Tabi’ai da Tabi’ut Tabi’in, Wannan
shi ne abin da nassoshin Alkur’ani
mai girma da Sunnah mai daraja ke
tabbatarwa. Shaikhul Islam Ibnu
Taimiyah ya ce cikin Majmuu’ul
Fataawaa 24/202:-
(()).
Ma’ana: ((Amma wannan da Sunnah
ta bayyana gare shi, sannan ya yi
zaton cewa waninta ya fi ta alheri,
to shi dan’bidi’ah ne, kai kafiri ne
ma)).
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
(()).
Ma’ana: ((Wanda ya bar nakalin da
aka gaskata daga mai fada wanda
yake ma’asuu’mi, sannan ya bi
nakalin da ba a gaskata ba daga
mai fadan da ba ma’asuu’mi ba,
hakika ya bace bata mai nisa)).
Allah Ya taimake mu Ya dora mu a
kan daidai har kullum. Ameen.


WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH. BA'ABARIN INGAN TACCEN HADISI SABODA YA SABAWA MAZAHABA
An Rubuta Ranar 08/11/17
Category :- Sulaiman Ibn Hujjah

0 Rate upStar
Share: F T G
Babu Jawabi A Wannan Darasin, Ya Kamata Ka Rubuta. Jawabi AQarkashin: BA'ABARIN INGAN TACCEN HADISI SABODA YA SABAWA MAZAHABA

SUNNAH
* SUNNAH (40/42)
Yadanganci Hadisan Annabi (s a w) Da Bin Tafarkinsa, Allah Ya Kara Tabbatar Da Mu Akan Sunnah.
RUBUTUTTUKAN MALUMA
* Dr Ibrahim Jalo Jalingo (10/11)
Rubututtuka , Daga Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.
* Dr. Jamilu Zarewa (136/142)
Fatawowi Daga Dr. Jamilu Zarewa
* Dr. Mansur Ibrahim Sokoto (10/10)
Rubutuka, Daga Dr. Mansur Ibrahim Sokoto
* Sheikh Aliyu Said Gamawa (2/2)
Rubutuka Daga, Sheikh Aliyu Said Gamawa
BIDI'A
* BIDI'A (17/19)
Bidi'a Shine Abin Da Manzon Allah (s a w) Bai Yarda Da Shi Ba. Allah Ya Tsaremu Daga Tsarrin Bidi'a.
ISLAMIC
* ISLAMIC (42/43)
Bangaren Addinin Musulunci, Hukunce - Hukuncen Addinin Musulunci Da Sauransu.
BANGAREN MATA
* BANGAREN MATA (29/29)
Domin Hukunce - Hukunce Da Suka Shafi 'yan Uwa, Iyaye Mata. A Shari'a
BANGAREN WEBSITE
* BANGAREN WEBSITE (6/13)
Domin Koyarda Website Da Blog Kamar, Wordpress, Xtgem, Blogger,
INTERNET & ANDROID
* INTERNET & ANDROID (12/14)
Kamar Fasahar Internet ,Android, Java, Da Sauran Abubuwan Da Suka Shafi Yanar Gizo.

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 21 user
This Week : 177 user
This Month : 459 user
Total all : 185512 visitors
LAST PAGES

Teya Salat



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: