Lamborghini Huracán LP 610-4 t

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

LATEST NEWS

LABARAI A TAKAICE

*LABARAI A TAKAICE* *Shugaban hukumar Alhazai ta Kasa, Abdullahi Mohammed ya bayyana cewa za a fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga ranar 21 ga watan Yulin 2018.* *Abdullahi ya ce za a fara da maniyyatan jihar Kogi ne. Sai dai kuma a jawabin sa bai fadi ko daga wace filin jirgin sama ne za su tashi ba.* *Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnonin jam’iyyar sa ta APC a fadar Aso Rock kan lamuran da kafafen labaru su ka yada na da nasaba da duba batutuwan jam’iyyar sa ta APC.* *Gwamnonin da a ka gani tare da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasar Abba Kayari, sun hada da Abdul’aziz Yari na Zmafara, Badaru Abubakar na Jigawa da Atiku Bagudu na jihar Kebbi. Taron dai na zuwa ne kwana daya bayan wasu ‘yan APC karkashin Buba Galadima sun aiyana kafa sabuwar tafiya a cikin jam’iyyar.* *Duk da haka bincike daga bisani ya nuna ba lalle kan wannan lamari shugaban ya gana da gwamnonin ba.* *Hankalin masu sharhi kan siyasar Najeriya ya koma jihar Ekiti ta kudu maso yammacin kasar don shirin zaben gwamnan jihar ranar 14 ga watan nan na Yuli.* *Ekiti dai ita kusan ita kadai ta rage a yankin karkashin mulkin babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP wanda ya sanya gwamnan jihar da zai bar gado Ayo Fayose yin zarge-zarge da dama na nuna shirin karbe jihar zuwa APC mai mulki.* *Fayose dai ya dage inda ya mara baya ga mataimakin Kolapo Olusola ya samu tikitin takara a inuwar PDP. Jagororin PDP da sauran magoya baya sun yi gangami a babban birnin jihar Ado Ekiti, don nemawa dan takarar su goyon baya.* *APC karkashin dan takarar ta Kayode Fayemi tuni ta gudanar da irin wannan gangamin da kuma watsi da zargin PDP da cewa ba shi da tushe. Zaben dai zai zama tamkar zakararan gwajin dafi ga babban zaben a Najeriya a Febrerun badi.* *An yi jana’izar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Mallam Adamu Ciroma wanda Allah ya yiwa rasuwa bayan fama da jinya a Abuja ya na mai shekaru 84. Mallam Adamu Ciroma dai na kan gaba cikin wadanda su ka shahara a lamuran siyasar Najeriya a jamhuriya ta biyu kuma ya rike ministan kudi a farkon gwamnatin farar hula ta Obasanjo.* *A bara a lokacin rufe tafsiri a masallacin Othman Bin Affan a anguwar Wuse 2, Mallam Adamu Ciroma ya yi jawabi mai kada zuciya da ya yi kama da ban kwana a masallacin da yakan halarci sallar jumma’a da tafsiri.* *Ciroma ya ce wannan jawabi da ya gabatar shine “NA KARSHE”An yi sallar jana’izar marigayin a masallacin Annur da ke Wuse 2 a Birnin Abuja* *Sojojin mabiya gwamnatin Bashar Al’Asad na Sham sun ci gaba da barin wuta a yankin Daraa na kudanci inda a ka ga hayaki ya turnuke sararin samaniya. Jiragen saman Rasha sun yi ta barin boma-bomai kan ‘yan hamaiya inda cikin sa’o’I 15 su ka kai hari sau 600.* *Kakakin ‘yan hamaiya na Daraa Hussein Abazeed ya ce ruwan boma-bomai ya hana ma damar ajiye wadanda su ka samu raunuka a inda ya dace don kula da su.* _*Ibrahim Baba Suleiman*_ _*Jibwis Social Media*_ _*22-Shawwal-1439*_ _*06-July-2018.*_
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH. LABARAI A TAKAICE
An Rubuta Ranar 06/07/18
Category :- LABARAI

0 Rate upStar
Share: F T G
Babu Jawabi A Wannan Darasin, Ya Kamata Ka Rubuta. Jawabi AQarkashin: LABARAI A TAKAICE

SUNNAH
* SUNNAH (40/42)
Yadanganci Hadisan Annabi (s a w) Da Bin Tafarkinsa, Allah Ya Kara Tabbatar Da Mu Akan Sunnah.
RUBUTUTTUKAN MALUMA
* Dr Ibrahim Jalo Jalingo (10/11) On: 1
Rubututtuka , Daga Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.
* Dr. Jamilu Zarewa (136/142)
Fatawowi Daga Dr. Jamilu Zarewa
* Dr. Mansur Ibrahim Sokoto (10/10)
Rubutuka, Daga Dr. Mansur Ibrahim Sokoto
* Sheikh Aliyu Said Gamawa (2/2)
Rubutuka Daga, Sheikh Aliyu Said Gamawa
BIDI'A
* BIDI'A (17/19)
Bidi'a Shine Abin Da Manzon Allah (s a w) Bai Yarda Da Shi Ba. Allah Ya Tsaremu Daga Tsarrin Bidi'a.
ISLAMIC
* ISLAMIC (42/43)
Bangaren Addinin Musulunci, Hukunce - Hukuncen Addinin Musulunci Da Sauransu.
BANGAREN MATA
* BANGAREN MATA (29/29)
Domin Hukunce - Hukunce Da Suka Shafi 'yan Uwa, Iyaye Mata. A Shari'a
BANGAREN WEBSITE
* BANGAREN WEBSITE (6/13)
Domin Koyarda Website Da Blog Kamar, Wordpress, Xtgem, Blogger,
INTERNET & ANDROID
* INTERNET & ANDROID (12/14)
Kamar Fasahar Internet ,Android, Java, Da Sauran Abubuwan Da Suka Shafi Yanar Gizo.

Online: Guests: 2




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 42 user
This Week : 193 user
This Month : 275 user
Total all : 185328 visitors
LAST PAGES



SULAIMAN IBN HUJJAH
禄HADA LOGO ANAN

Download
Enter Your Text:

Select Style: