
WAYE DR IBRAHIM JALO JALINGO?
”
Dr Ibrahim Muhammad Jalo Jalingo an Haife shi a garin Muri dake Jahar Taraba, yayi karatun sa na allo da na Addini a gun Mahaifinsa da Mahaifiyarsa, yayi Primary da Secondary a Garin Sung, yayi diploma a Jami’ar Bayaro kano, ya wuce Jami’ar Musulunci ta Madina yayi Karatu a Fannin Fikhu.
”
Kuma kafin ya tafi Jami’a ya sauke littafin Ahlari, Ishmawi, Iziya, Risala, Askari, Muktasar.
”
A bangaran wakoki ya sauke littafin Daliya, Shariya, muktaril shi’iri jahili, Mukamatul hariri.
”
A bangaran Nahau ya sauke Addurusin Nahawiya, Nahaul wadhi, Alfiyatu bin Malik.
”
Duk takamar ka da ka karanta Nahau ba ka wuce Alfiyatu bin malik ba. To tun Dr be je Jami’a ba ya karanta.
”
Duk takamarka ka karanta Fikhu baka wuce Muktasar Khlili ba. Dr ya karanta tun be je Jami’a ba.
”
Duk takamarka ka karanta lugga baka wuce Mukamatul hariri ba. Dr ya karanta tun be je Jami’a ba.
”
Dr Ibrahim Jalo Jalingo yayi degree din sa na 1 a Fannin Fikhu, Yayi Degree na 2 a Fannin Fikhu, Yayi Degree na 3 wato P.H.D a Fannin Fikhu.
”
A tsarin karatun Jami’ar Musulunci ta Madina ba a daukar mutum yayi masters sai yana da Mumtazi ma’ana sai yanada 4.75 a madadin 4.5 a Jami’oin kasar mu nigeria, kuma a cikin wayanda suke da 4.75 ma sai an sake musu jarabawa don a kara tace a reraye kafin mutum ya samu daman yin degree 2, shi ma ba za a bawa mutum daman yayi degree 3 ba wato P.H.D sai an tabbatar yanada Inmtiyadi zuwa sama.
”
Wannan shine Dr Ibrahim Muhammad Jalo Jalingo.
”
Ka gaya min ta yaya Jahili zai tsallake wannan Matsayin har ya kai Dr ba a gane Jahili ba ne sai kai dan tashi zaka gane?
Wannan bayanin ya fito ne daga marigayi Sheik Dr. Alhassan Sa’id Adam Jos.
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
WAYE DR IBRAHIM JALO JALINGOCreated at 05/13/18
Category
Waye Dr Ibrahim Jalo Jalingo

0
Rate up
Star
Share: