Polly po-cket

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

BLOG

AN YI KIRA GA GWAMNAN KANO DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE AKAN BATUN KARBE MAKARANTA DA FILAYE MALLAKAR MASALLACIN SHEIKH JAFAR ADAM DAKE SABUWAR GANDU.

AN YI KIRA GA GWAMNAN KANO DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE AKAN BATUN KARBE MAKARANTA DA FILAYE MALLAKAR MASALLACIN SHEIKH JAFAR ADAM DAKE SABUWAR GANDU.
AN YI KIRA GA GWAMNAN KANO DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE AKAN BATUN KARBE MAKARANTA DA FILAYE MALLAKAR MASALLACIN SHEIKH JAFAR ADAM DAKE SABUWAR GANDU. Wannan kira ya fito ne daga bakin Babban Limamin Masallacin Jumu'a na Uthman Bin Affan dake Kofar Gadon Kaya Sheikh, Dr. Abdallah Uthman Gadon Kaya a jiya lokacin da yake gabatar da Hudubar Sallar Idi a farfajiyar Masallacin Sabuwar Gandu dake cikin Birnin Kano. Tunda farko Shehin Malamin ya fara isar da sakon ne ga Mai Girma Gwamna da kalamai na gimamawa da mutuntawa, sannan yace ya kamata Mai Girma Gwamna yayi amfani da Shekarunsa, Dattijontakarsada iliminsa wajen samarwa kansa kyakkyan tarihi kar ya jefa kansa cikin rikici na addini wanda zai haifar masa da babbar matsala a tafiyarsa ta siyasa. Malam ya cigaba da cewa ya Mai girma Gwamna ka sani cewa ba'a sulhunta mutane da karfin Mulki ko amfani da wata dama ta siyasa, kadai dai ana sulhu ne da adalci da kuma sanin ya kamata. Kazalika Malam yayi kira ga Mai Girma Gwamna akan kar ya bari wasu yan tsirarun mutane su zuga shi su hada shi fada da Ahlussunnah saboda wannan fadan ba nasa bane, fada ne da yafi karfinsa don haka Mai Girma Gwamna yayi hattara. Ya Mai Girma Gwamna a matsayinka na Khadimul Islam wannan makaranta ko ba mallakar Masallaci ba ce ai kai mai iya siyenta ne ka mallaka masa domin ko ba komai za'a karantar da al'umar musulmi Alqur'ani da Sunnar Annabi S.A.W balantanama Makarantar da Filayen dukkaninsu Mallakar Masallacin ne, don haka ayi adalci kar a fada ramin da baza a iya fitowa ba. Matukar ba ayi mana adalci ba wajen dawo mana da Makarantarmu da filayenmu ba Wallahi Thumma Tallahi zamu yi amfani da dukkanin damar da Allah Ya bamu wajen daukar matakin da ya dace domin muma yan kasa ne muna da yancin muyi Addininmu ba tare da tsangwama ba. Bayan haka Malam yace a tarihin duniya babu wani Shugaba na Siyasa ko Sarkin gargajiya da zaiyi rigima da Ahlussunnah kuma ya kwashe lafiya, don haka idan Mai Mirma Gwamna ya manta da wannan tarihin ya je ya kakka6e kundi ko kuma ya tambayi na kusa dashi su bashi labari. Daga karshe Shehin Malamin ya gabatar da addu'oi akan duk wadanda suke da hannu wajen kokarin karbe wannan makaranta da filaye ga wannan Masallaci idan masu shuryiwa ne Allah Ya shiryesu idan kuma ba masu shiryiwa bane Allah Ya saka su cikin Kunci, Ya kar6e musu duk wata dama da suke da ita Ya kuma raba su da duk wani jin dadi duniya da lahira. Lawal Mamman Bilbis
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH. AN YI KIRA GA GWAMNAN KANO DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE AKAN BATUN KARBE MAKARANTA DA FILAYE MALLAKAR MASALLACIN SHEIKH JAFAR ADAM DAKE SABUWAR GANDU.
Created at 06/17/18
Category LABARAI

0 Rate upStar
Share: F T G
Comments: AN YI KIRA GA GWAMNAN KANO DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE AKAN BATUN KARBE MAKARANTA DA FILAYE MALLAKAR MASALLACIN SHEIKH JAFAR ADAM DAKE SABUWAR GANDU.
Photo
Shuraih99
06/22/18

yadda zaka hada wapka wepsite sak irin na Tipsbank24.com kashi na daya 1 headtags

Assalam
Yau dai ina tafe maku da yadda zaku design na wepsite naku sak irin Tipsbank24.com

img


danna nan kaga cikakken post din

Photo
Shuraih99
06/22/18

yadda zaka hada wapka wepsite sak irin na Tipsbank24.com kashi na daya 1 headtags

Assalam
Yau dai ina tafe maku da yadda zaku design na wepsite naku sak irin Tipsbank24.com

img


http://keffians.xtgem.com/Blog/__xtblogentry/11602348-hada-wepsite-code-din-headtags-na-tipsbank24.com-kashi-na-daya-1#xtblog

ABOUT ADMIN
Sulaiman     1
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click to Call MeClick to Sms Me




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 8 user
This Week : 9 user
This Month : 8 user
Total all : 91904 visitors
LAST PAGES