
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai
Daga Ibrahim Baba Suleiman
A yanzun nan muka samu labarin shugaban kungiyar Izala ta jihar Plateau ustaz Ibrahim Barikin Ladi ya koma gida yana cikin iyalansa a yanzu haka.
Lamarin ya faru ne bayan sa'ar juyawa baya da yayi Allah ya taimake shi ya fita a guje kuma yayi sa'ar shiga wata makarantar 'yan sanda (Staff Collage) inda ya samu mafaka a wajen.
A zantawar da wakilin mu Ibrahim Baba Suleiman yayi da shi, ya tabbatar mana cewa Allah ya kwace shi, ya dawo dashi cikin iyalansa, amma duk wayoyinsa suna hannun 'yan ta'addan, kuma an kashe mutum biyu cikin jami'an tsaron da yake tare dasu.
Ustaz Ibrahim Barikin Ladi ya kuma ce a isar masa da dubun dubatan gaisuwa ga Al'umma wadanda sukayi ta aike masa da addu'oi, kuma Allah ya karba dan gashi ya tsira da ransa.
Jama'a kuma Allah ya saka muku da alkhairi.
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
Shugaban Kungiyar Izala ta Jihar Plateau Ustaz Ibrahim Barikin Ladi Ya Koma Gida Yana Cikin Iyalansa A Yanzu Haka.Created at 06/25/18
Category
LABARAI
,
Sanarwa

0
Rate up
Star
Share: