
A FAKAICE MAGOYA BAYAN C.A.N SUN AMINCE DA CEWA SU NE KE KASHE SHANUN MUSULMI:
1. A cikin 'yan kwanakin nan bayanai da ake ji daga gidajen radio, ake kuma ji da gani daga gidajen talabijin, ake kuma karantawa daga jaridu, da kafafen sada zumunta; watau bayanai da suke fitowa ta bakuna, da alkaluman magoya bayan kungiyar CAN, wadannan bayanan suna tabbatar da cewa: A dai fakaice su wadannan masu tarbiyyantuwa da tarbiyyar Kungiyar CAN sun yarda da cewa su ne ke kashe shanun al'ummar Musulmi; hujjarsu ta yin hakan kuwa ita ce: su a ganinsu al'ummar musulmi makiyaya, rayukansu, da dukiyarsu ba su cancanci samun kariyar da constitution din Nigeria ya ba wa ko wane dan Nigeria ba!
2. Lalle gaskiya za ta cigaba da bayyana ko ba dade, ko ba jima; In sha Allahu Ta'aalaa kamar yadda yanzu suka yarda da cewa su ne ke kashe shanu, nan gaba kadan za su yarda su fito fili su gaya wa duniya cewa: su ne ke kashe makiyaya, su ne kuma ke tare manyan hanyoyi suna kashe dukkan Musulmin da ke cikin motocin da suka tsayar a bisa zalunci, da tsananin kiyayya.
Allah Ka tsare Nigeria, da 'Yan Nigeria daga sharrin kungiyar CAN. Ameen.
Daga: Dr Ibrahim Jalo Jalingo.
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
A FAKAICE MAGOYA BAYAN C.A.N SUN AMINCE DA CEWA SU NE KE KASHE SHANUN MUSULMICreated at 06/30/18
Category
islamic
,
LABARAI

0
Rate up
Star
Share: