
Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe
.....An kuma Umurci Iimamai su ware lokaci domin wayar da kan Al'umma akan katin zabe (PVC)
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban kungiyar Wa'azin musulunci, mai Da'awar tuge bidi'ah, ta tsaida Sunnar Annabi Muhammadu (S), Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga shugabannin addini, Limamai da sauran masu fada aji a dukkan matakai, da su dinga wayar da kan Al'ummar musulmi a masallatai, makarantu da sauran wuraren tarukan addini akan muhimmancin yankan katin zabe c(PVC) a wannan lokaci da muke ciki.
Sheikh Bala Lau yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da wakilin mu 'Ibrahim Baba Suleiman' ta wayar tangaraho a safiyar laraba.
Shehin Malamin yace, duk wanda yasan bai mallaki katin zabe ba, yayi kokari ya mallaka, domin yankar katin zabe a wannan lokaci ya zama sabon salo, idan kuwa har kuka saki jiki bakuyi ba, to yana da kyau ku ankara domin samun shugabanni na gari wadanda muke sonsu, suma suke sonmu.
Kazalika akwai wadanda suka mallaki katin zabe (PVC) amma basa zuwa rumfar zabe domin kada kuri'a, wanda hakan zai maida mu baya, musamman akan shirin da abokan zaman mu sukeyi domin su mallaki katin zabe, dan haka a daure a kada kuri'u ranar zabe ba tare da gajiyawa ba.
A karshe Sheikh Bala Lau ya umurci Shugabannin jihohi da su umurci shugabannin kananan hukumomi su wayar da kan Al'umma a yankunan su a dukkan matakai na shugabanci da sauran mabiya. Kazalika Sheikh Lau ya sake umurtan Limaman Juma'a da su ware lokaci a cikin hudubobin su na juma'ar dake gaban mu, domin fadakar da Al'umma akan muhimmancin yankan katin zabe.
Allah ya zaba mana shugabanni na gari, ya gyara mana kasar mu, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a kasa. Amin
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabeCreated at 07/04/18
Category
LABARAI

0
Rate up
Star
Share: