Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

BLOG

Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe

Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe
Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe .....An kuma Umurci Iimamai su ware lokaci domin wayar da kan Al'umma akan katin zabe (PVC) Daga Ibrahim Baba Suleiman Shugaban kungiyar Wa'azin musulunci, mai Da'awar tuge bidi'ah, ta tsaida Sunnar Annabi Muhammadu (S), Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga shugabannin addini, Limamai da sauran masu fada aji a dukkan matakai, da su dinga wayar da kan Al'ummar musulmi a masallatai, makarantu da sauran wuraren tarukan addini akan muhimmancin yankan katin zabe c(PVC) a wannan lokaci da muke ciki. Sheikh Bala Lau yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da wakilin mu 'Ibrahim Baba Suleiman' ta wayar tangaraho a safiyar laraba. Shehin Malamin yace, duk wanda yasan bai mallaki katin zabe ba, yayi kokari ya mallaka, domin yankar katin zabe a wannan lokaci ya zama sabon salo, idan kuwa har kuka saki jiki bakuyi ba, to yana da kyau ku ankara domin samun shugabanni na gari wadanda muke sonsu, suma suke sonmu. Kazalika akwai wadanda suka mallaki katin zabe (PVC) amma basa zuwa rumfar zabe domin kada kuri'a, wanda hakan zai maida mu baya, musamman akan shirin da abokan zaman mu sukeyi domin su mallaki katin zabe, dan haka a daure a kada kuri'u ranar zabe ba tare da gajiyawa ba. A karshe Sheikh Bala Lau ya umurci Shugabannin jihohi da su umurci shugabannin kananan hukumomi su wayar da kan Al'umma a yankunan su a dukkan matakai na shugabanci da sauran mabiya. Kazalika Sheikh Lau ya sake umurtan Limaman Juma'a da su ware lokaci a cikin hudubobin su na juma'ar dake gaban mu, domin fadakar da Al'umma akan muhimmancin yankan katin zabe. Allah ya zaba mana shugabanni na gari, ya gyara mana kasar mu, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a kasa. Amin
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH. Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe
Created at 07/04/18
Category LABARAI

0 Rate upStar
Share: F T G
This post has no comments - be the first one! Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe
ABOUT ADMIN
Sulaiman     1
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click to Call MeClick to Sms Me




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 15 user
This Week : 16 user
This Month : 15 user
Total all : 91911 visitorsUnited States
LAST PAGES