Duck hunt

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

BLOG

LALLE NE MU GUJE WA NUNA BUTULCI GA NI'IMOMIN ALLAH:

LALLE NE MU GUJE WA NUNA BUTULCI GA
NI'IMOMIN ALLAH:
LALLE NE MU GUJE WA NUNA BUTULCI GA NI'IMOMIN ALLAH: 1. Lalle wajibi ne mu al'ummar Nigeria mu kara gode wa Allah, kada mu nuna wa ni'imominSa da ya yi mana butulci; saboda dalilin hamayyar siyasa, ko kiyayyar addini, ko abin da ya yi kama da haka. 2. Abin mamaki ne matuka a ce mutanen da tun farkon kafuwarsu babu abin da suka sanya a gaba fiye da neman wargaza Nigeria, da cutar da al'ummar Arewacin Nigeria, da nuna cewa Musulmi 'Yan Arewacin Nigeria ba su da hakkin jagorantar Nigeria cikin kwanciyar hankali, da kunna fitinu iri-iri nan da can; abin mamaki ne a ce irin wadannan mutane wai su ne suka hadu a Abuja jiya Laraba 18/7/2018 da sunan neman Gwamnatin Nigeria ta tsaida kashe-kashen da galibi su wadannan mutanen su ne ke daukar dawainiyarsu a fakaice!! 3. Yanzu dai wai fa Chief Ayo Adebanjo ne shugaban fandararriya, kuma muguwar kungiyar nan ne ta Afenifere; watau kungiyar Yarbawa zalla, da kuma Chief John Nwodo ne shugaban Ohanaeze Ndigbo; watau shugaban kare muradun Iyamurai, da kuma Chief Edwin Clark shugaban 'Yan Neja Delta watau Pan Niger Delta (PANDEF), wai wadannan mutanen ne suka taru a Abuja jiya Laraba suke yin kira ga Gwamnatin Nigeria da ta tsaida kashe-kashen da ake yi a wasu yankunan Kasar nan! Suna cewa wai kashe- kashen da ke faruwa a yanzu yawansu ya zarce irin wadanda suka taba faruwa a gwamnatocin baya!! 4. Sannan lalle abin takaici ne matuka; saboda kawai hamayya irin ta siyasa a ce Prof. Ango Abdullahi shugaban NEF watau Northern Elders Forum ya shiga cikin wadannan kungiyoyi da suka shahara wajen kulla wa Nigeria sharri, suka shahara wajen cutar da 'Yan Arewa da kashe su, da lalata dukiyarsu; saboda gilli da yawan zalunci! 5. Lalle wajibi ne mu al'ummar Nigeria mu kara kaskantar da kai a gaban Allah, mu gode masa a kan Ni'imar da ya yi mana ta kawar da barazanar yan bokoharam ta share wanzuwar Nigeria gaba daya a doron Duniya, sannan kuma wajibi ne mu jinjina wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda irin kyakkyawan jagorancin da ya nuna har aka sami kai wa ga irin wannan nasara ta tsaida wannan barazanar. Sannan kuma ya kara samun nasara cikin bangarori daban daban na gina kasa, wanda a jiya ma aka yi bukin dawo da kamfanin jiragen saman Nigeria, bayan kashe kamfanin gaba dayansa a 2003. 6. In sha Allahu Ta'alaa wadannan kashe kashe da gurbatattun 'yan Kasa ke yi, ko ke sanyawa a yi; watau gurbatattun 'yan kasa kamar su kungiyar CAN, da kungiyoyin kabilanci da bangaranci, da masu fashin shanu, da masu garkuwa da mutane, da masu fashi da makami, da kungiyoyin asiri, da kungiyoyin tarzoma, da gurbatattun 'yan siyasa; in sha Allah Ta'alaa su ma za a kawo karshen balbalin bala'insu ya koma tarihi kamar yadda bokoharam suka koma. Allah Ka tausaya wa al'ummar Nigeria Ka sanya ta cikin bayinKa masu gode maKa a kan ni'imominKa mara iyaka. Ameen. Rubutawa: Dr Ibrahim Jalo Jalingo
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH. LALLE NE MU GUJE WA NUNA BUTULCI GA NI'IMOMIN ALLAH:
Created at 07/21/18
Category islamic , LABARAI

0 Rate upStar
Share: F T G
This post has no comments - be the first one! LALLE NE MU GUJE WA NUNA BUTULCI GA NI'IMOMIN ALLAH:
ABOUT ADMIN
Sulaiman     1
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click to Call MeClick to Sms Me




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 12 user
This Week : 13 user
This Month : 12 user
Total all : 91908 visitorsUnited States
LAST PAGES