Polly po-cket

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

BLOG

AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM

AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM
AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM -----+-+++++++++++----------------------- 1. Ana amfani da kubewa wajen maganin ciwon sugar wato Diabetes. Saboda abinda ake kira (fiber ) a cikinta, na amfani wajen daidaita yawan suga a cikin jiki, wandakuma ke rage karfi ciwon sugar ko ma maganinsa. 2. Masu ciki kan iya amfani da kubewa domin ingancin lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki (cells) da kuma ( folates) don haka kubewa na hana haihuwar jariri mai dauke da wasu nakasu a jikinsa kuma na sa jaririn ya girma a ciki kuma da koshin lafiya yadda ake so. Haka kuma jaririn da ke ciki zai iya amfana da dimbin Vitamin C dake cikin kubewa domin kare lafiyarsa. 3. Kubewa na maganin ciwon koda. Wani bincike daga jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da wannan. Binciken. Ya nuna cewar wadanda suke ci ko shan kubewa a kullun sun nuna nasarar rashin lalacewar koda musamman wadanda ke da ciwon sugar domin kusan kasha 50 na masu matsalar koda sun samu matsalar ne saboda suna da ciwon sugar. 4. Kubewa na kara lafiyar dubura (colon) wato karshen babban hanji.yana wanke hanji da tumbi sosai don haka yana maganin kumburin ciki. Kuma Vitamin A da ke cikin kubewa na taimakawa lafiyar wani abu kamar majina (Mucous membranes) na cikin babban hanji. 5. Kubewa na maganin Asthma da wasu cututtukan numfashi. Yana dauke da Vitamin C da ke taimakawa hanyoyin numfashi. 6. Kubewa na kara ingancin fatan jikin mutum yay i laushi da santsi kamar yaukin kubewa. Ka ga mutum kullun kamar yaro ko yarinya a fatarsa. Yana kuma taimakawa wajen mayar da fatar da ta lalace (Meosis). 7. Yana matukar maganin Anaemia wato karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfaani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har yayi maka lahani ba (blood coagulation). 8. Yawan sha ko cin kubewa na matukar rage nauyin jiki ga wadanda suke jin kiba ya musu yawa. Naku: Jamilu Gora
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH. AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM
Created at 07/23/18
Category Kiwan Lafiya

0 Rate upStar
Share: F T G
This post has no comments - be the first one! AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM
ABOUT ADMIN
Sulaiman     1
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click to Call MeClick to Sms Me




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 7 user
This Week : 8 user
This Month : 7 user
Total all : 91903 visitors
LAST PAGES