ibnhujjah
Assalama Alaikum Jama’a barkanmu da sake haduwa a cikin wannan shiri na
WORDPRESS kashi na biyu.
Idan mai karatu bai manta ba muntsaya ne inda mukagama
INSTALLING din wordpress idan kuma baka karanta zaka iya bin wannan link din
YANDA ZAKA GINA WEBSITE A WORDPRESS CIKIN SAUKI
MENENE THEME
Themes shine gin shiki na wordpress domin dukkan wani website dinda kagani a wordpress an hada shine daga themes. Da themes zaka yi ampani wajen tsara website dinka zuwa duk wani kalan design dinda kakeso. A wordpress zaka iya gina website kalan duk wanda kaga dama kamar Chatting Site, Download Site, News Site. Youtube Downloader Site da sauransu domin kuwa zaka iya juya website dinka na wordpress zuwa duk yanda kaga dama amma ta hanyar ampani da Theme da kuma Plug-ins.
Kenan a takaice dai theme shine abu mapi ampani a site din wordpress.
Da farko Ku Sami Theme Me Kyau Ku Sauke A Wayarku.
bayan kun saukar da Theme din saiku je website dinku da kukayi register wato inda kukayi misali
www.ibnhujjah.arewaphp.cf/wp-admin saiku saka username da kuma password dinku bayan ya bude saiku kara wannan a gaban sunan shafinku
theme-install.php kunga kenan zai dawo kamar haka misali
www.ibnhujjah.arewaphp.cf/wp-admin/theme-install.php
In ya bude zakuga
UPLOAD THEME to saiku danna kai zakaga inda zaku dauko abu daga cikin memory idan kuka za6i wannan theme dinda kuka dauko saiku danna upload amma idan kana ampani da Java Phone ne gwanda kayi ampani da Uc Browser saboda shine zai baka damar daura theme din bayan ya hau saiku danna kan
Activate theme daga nan saiku ziyarci shafin ku zaku sha mamaki.
Canza logo da sauran bayanin theme din saiku rubuta sunansitedinka.arewaphp.cf/wp-admin/theme-editor.php to anan zaku gyara
Header-default.php da kuma
footer.php shikenan kun gama hada shafin ku sauran kawai ku ringa posting upload. Da Sauransu.