Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

* ibnhujjah ' YAN BIDI'AH HAR KULLUM CUTAR DA MUSULUNCI SUKE YI: 1. Abin da 'Yan bidi'ar Bokoharam suka yi na kin sakin wata yarinya kirista da hujjar cewa: taki musulunta, lalle yana daga cikin abin da son zuciya da jahiltan hakikanin Musulunci ke janyo musu. 2. Lalle bidi'ar dukkan wasu 'yan bidi'ah tana ginuwa ne a kan abu biyu: Jahilci murakkabi, da kuma son zuciya, su ma kuma 'yan bokoharam wannan shi ne halinsu. 3. Tabbas ba don 'yan bokoharam jahilai ne murakkabai masu kuma cike da son zuciya ba, lalle da sun san cewa: tun farkon fari ma haramun ne a kansu su shigo cikin makarantar Dapchi su kwashe daliban da ke cikinta; musulminsu da kiristocinsu, to amma saboda son zuciyarsu da kuma jahilcinsu ga hakikanin Musulunci sai suka zaci cewa yin abin da suka yin wata ibadah ce da ake neman lada ta hanyar aikata ta! 4. Tabbas kin sakin wannan yarinya kirista da 'yan bidi'ar bokoharam suka yi, sun kara wa yarinjar da iyayenta daraja da kima ne a idanun da yawa daga cikin mahankaltan duniya, sun kuma kara shafawa Musulunci da Musulmi bakin fenti ne a idanun da yawa daga cikin azzaluman duniya. Allah Ka tausaya mana Ka raba mu da sharrin bidi'ah da ma'abutanta. Ameen.
2018-03-25 13:46 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 14 user
This Week : 612 user
This Month : 613 user
Total all : 94020 visitorsUnited States
LAST PAGES

Disneyland 1972 Love the old s