The Soda Pop

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

* ibnhujjah IDI
- Idi shine bikin da sharia ta tanadar wa musulmai a madadin bukukuwan maguzanci ko al’adun da sharia ba ta yarda da su ba.
- Sallar Idi sunna ce mai karfi. Ba shi kyautuwa mutum ya bar ta ba tare da larurar da ta sha gabansa ba.
- Sunna ta nuna a fita bayan gari ne a yi sallar idi in dai ba akwai larura ba.
- Ana so kowa ya fita zuwa sallar idi da suturasa mafi kyau )sababbi ko wankakku(.
- Ana so mata da yara da tsofaffi su fita. Har da mata masu haila. )Amma ba za su yi sallar ba(.
- Wadanda basu da suturar fita anguwa babu laifi su ara a wajen kawaye ko ‘yan uwa ko abokan zamansu.
- Ana yin sallar idi ne da hantsi, an so a jinkirta sallar azumi kamar yadda kuma aka so a yi ta layya da wuri.
- Liman zai yi wa mutane sallah raka’a biyu da huduba a bayan sallar.
- Manzon Allah )SAW( ya kasance yana karanta ) Suratul "kaf ( da ) "kamar ( a sallolinsa na idi.
- Bayan sallar manzon Allah )SAW( yana yin huduba guda daya.
- Mustahabbi ne sauraron hudubar sallar idi.
- Liman bai yin nafila kafin ko bayan sallar idi. Amma an samo daga magabata sukan yi nafila kafin sallar idi da bayan ta a filin idin ko a hanya ko a masallacin gari.
- Ana son mutane su yawaita kabarbari tun daga wayewar garin sallah har yammacin karshen kwanakin tashreeq. Karamar Sallah ba ta da kwanakin Tashreeq
- An so a tafi filin idi a kafa kuma a canza hanya a yayin dawowa gida
- An so wanda zai yi layya ya kame baki daga cin wani abu har sai an yanka dabbarsa sannan ya ci daga sashen namanta
- Akwai kashedi da annabi )SAW( ya yi ga wanda ke da halin layya amma ya ki yi. )cewa kar ya kusanci filin idin musulmi(
- Idan idi ya hadu da juma’a, wanda ya halarci idi to wajabcin juma’a ya fadi a kansa. Amma halartar duka idi biyun )idi da juma’a( ya fi falala.
- Wanda kuma ya dauki sassaucin bai yi laifi ba. Amma zai yi azahar a gida ko a masallacin. anguwarsu shi kadai ko tare da ire-irensa.
- Wanda bai sami idi ba zai rama, sannan zai je juma’a a bisa wajabci.
- Babu laifi yi wa juna barka da sallah bisa abin da yake sananne a sharia.
- Babu laifi gudanar da sauran harkokin bikin sallar da al’adun da ba su saba wa shariar musulunci ba.
- A guje wa ganganci da ababen hawa da sunan murna.
- A guje wa fitar mata da yara barkatai.
- A guje wa sanya suturun da suka saba wa sharia da al’ada ta gari
ALLAH YA SA MU DACE
http://islamicforum.com.ng/idi
2018-06-14 13:59 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 291 user
This Week : 889 user
This Month : 890 user
Total all : 94297 visitors
LAST PAGES