The Soda Pop

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

* ibnhujjah MUSULUMCI BABBAR NI’iMA:
Babu wata ni’ima da tafi samun ni’imar
musulumci, wato duk wanda Allah ya qaddara
masa zama musulmi to ya godewa Allah bisa
wannan baiwa mai girma, kuma ya dage wajen
kara fahimta da neman sanin sakon da Annabi
(Saw) yazo dashi.
Ana fatan musulmi na kwarai ya tsarkake Allah
(twa) shi kadai cikin bauta, ya tsaya kan tafarkin
Annanbi (saw), daga nan ya dage da kokarin
ibada, sannan ya nisanci aikata miyagun aiyukan
zunubi.
Kowani musulmi ya sani akwai hakkoki akan sa
tsakanin sa da ubangiji kan ya bauta masa,
tsakanin sa da Annabi (saw) ya yi masa biyayya
cikin dukkan umarni da hani, sannan akwai hakkin
iyaye, iyalai, makwabta, dangin zumunta, tsirrai
da dabbobin ni’ima da ya mallaka. Dukkan
wadannan hakkoki ka sani za’a tambayeka akan
su, don haka mu kula wajen sauke hakkokin dake
kan mu, kuma muna karawa da ihsani cikin
mu’amalar mu.
Musulmi na kwarai zaka same shi mai kyak-
kyawan hali, mai umarni da aiyukan kwarai mai
hani akan miyagun aiyuka, mai son tsayawa kan
gaskiya, mai adalci da kiyaye amana, mai tsare
harshen sa daga munanan kalamai da aka hana,
mai saukin kai, mai tausayi da yafe laifi, mai
yawan alheri cikin tallafawa marayu, marasa gata,
nakasassu da tsofaffi maza da mata. Don haka
ne shi musulmi na kwarai ake gane shi da
natsuwar sa, ga kamun kai da rike mutumci.
Mu sani bayin Allah abin kyama ne musulmi ya
zamo mai girman kai, mai kwadayi, mai hassada,
mai yawan surutu da karya, mai gulma da
munafurci, mai rowa da yawan gori, mai zaman
kara zube ba neman ilimin addini da rayuwa, mai
yawon maula da matsawa mutane da nacin roko,
ko mai yawan aikin fasikanci, da mai zalunci na
zubar da jini ko cin dukiyar mutane ba bisa hakki
ba.
Dan uwa na mai daraja madallah da zamanka
musulmi a rayuwar ka. Ka sani dukkan halaye da
dabi’u da zasu cutar da kai an hana ka, kuma an
kwadaitar da kai zuwa ga dukkan abinda zai
amfane ka. Pls mu riki kyawawan halaye. Kuma
mu daina dukkan abin da zai zubar mana da
mutumci da abinda aka haramta mana.
Tabbas rayuwa mai dadi a duniya da lahira na
samuwa ga mai tsayawa kan dokokin musulumci,
kuma wanda Allah ya zabeshi da zama musulmi,
to shine ya samu aka tsarkake masa zuciyar sa
daga kazamtar kafirci, don haka ake so ana
kowanni musulmi yana yiwa wannan ni’ima
kwalliya da neman ilimi da yawan ibada.
2018-07-01 08:35 · Reply · (0)


Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 197 user
This Week : 795 user
This Month : 796 user
Total all : 94203 visitorsUnited States
LAST PAGES