80s toys - Atari. I still have

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

* ibnhujjah LALLE NE MU GUJE WA NUNA BUTULCI GA
NI'IMOMIN ALLAH:
1. Lalle wajibi ne mu al'ummar Nigeria mu
kara gode wa Allah, kada mu nuna wa
ni'imominSa da ya yi mana butulci; saboda
dalilin hamayyar siyasa, ko kiyayyar addini,
ko abin da ya yi kama da haka.
2. Abin mamaki ne matuka a ce mutanen da
tun farkon kafuwarsu babu abin da suka
sanya a gaba fiye da neman wargaza Nigeria,
da cutar da al'ummar Arewacin Nigeria, da
nuna cewa Musulmi 'Yan Arewacin Nigeria ba
su da hakkin jagorantar Nigeria cikin
kwanciyar hankali, da kunna fitinu iri-iri nan
da can; abin mamaki ne a ce irin wadannan
mutane wai su ne suka hadu a Abuja jiya
Laraba 18/7/2018 da sunan neman Gwamnatin
Nigeria ta tsaida kashe-kashen da galibi su
wadannan mutanen su ne ke daukar
dawainiyarsu a fakaice!!
3. Yanzu dai wai fa Chief Ayo Adebanjo ne
shugaban fandararriya, kuma muguwar
kungiyar nan ne ta Afenifere; watau kungiyar
Yarbawa zalla, da kuma Chief John Nwodo ne
shugaban Ohanaeze Ndigbo; watau shugaban
kare muradun Iyamurai, da kuma Chief
Edwin Clark shugaban 'Yan Neja Delta watau
Pan Niger Delta (PANDEF), wai wadannan
mutanen ne suka taru a Abuja jiya Laraba
suke yin kira ga Gwamnatin Nigeria da ta
tsaida kashe-kashen da ake yi a wasu
yankunan Kasar nan! Suna cewa wai kashe-
kashen da ke faruwa a yanzu yawansu ya
zarce irin wadanda suka taba faruwa a
gwamnatocin baya!!
4. Sannan lalle abin takaici ne matuka; saboda
kawai hamayya irin ta siyasa a ce Prof. Ango
Abdullahi shugaban NEF watau Northern
Elders Forum ya shiga cikin wadannan
kungiyoyi da suka shahara wajen kulla wa
Nigeria sharri, suka shahara wajen cutar da
'Yan Arewa da kashe su, da lalata dukiyarsu;
saboda gilli da yawan zalunci!
5. Lalle wajibi ne mu al'ummar Nigeria mu
kara kaskantar da kai a gaban Allah, mu gode
masa a kan Ni'imar da ya yi mana ta kawar
da barazanar yan bokoharam ta share
wanzuwar Nigeria gaba daya a doron Duniya,
sannan kuma wajibi ne mu jinjina wa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda
irin kyakkyawan jagorancin da ya nuna har
aka sami kai wa ga irin wannan nasara ta
tsaida wannan barazanar. Sannan kuma ya
kara samun nasara cikin bangarori daban
daban na gina kasa, wanda a jiya ma aka yi
bukin dawo da kamfanin jiragen saman
Nigeria, bayan kashe kamfanin gaba dayansa
a 2003.
6. In sha Allahu Ta'alaa wadannan kashe
kashe da gurbatattun 'yan Kasa ke yi, ko ke
sanyawa a yi; watau gurbatattun 'yan kasa
kamar su kungiyar CAN, da kungiyoyin
kabilanci da bangaranci, da masu fashin
shanu, da masu garkuwa da mutane, da masu
fashi da makami, da kungiyoyin asiri, da
kungiyoyin tarzoma, da gurbatattun 'yan
siyasa; in sha Allah Ta'alaa su ma za a kawo
karshen balbalin bala'insu ya koma tarihi
kamar yadda bokoharam suka koma.
Allah Ka tausaya wa al'ummar Nigeria Ka
sanya ta cikin bayinKa masu gode maKa a kan
ni'imominKa mara iyaka. Ameen.
Rubutawa: Dr Ibrahim Jalo Jalingo
2018-07-21 03:30 · Reply · (0)


Online: Guests: 1

ABOUT ADMIN
Sulaiman
Name: Sulaiman Aliyu Yahaya ( Ibn Hujjah )
State: Kano
Country: Nigeria

Click To Call MeClick To Sms Me

RUBUTA RA'AYINKA




Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 196 user
This Week : 794 user
This Month : 795 user
Total all : 94202 visitorsUnited States
LAST PAGES