ibnhujjah
Ina kuke masu amfani da wayar Android shin kunsan zaku iya fitar da amsar lissafi/math ta hanyar daukan hoton tambayar da wayar android sannan wayar ta fidda muku amsar dede, Abin babu wuya kawai idan kana da wayar android zaka iyayin hakan, sannan android din ya kasance yana da Camera mai kyau, domin kuwa kawai Lissafin zaka Rubuta ajikin Littafi ko wata takarda saika haska da wayarka, nan take zakaga ta baka amsa dede, inde har kayi Rubutun dede to insha Allah zaka samu amsa, yanzu abin da zakuyi kawai ku shiga Link dinnan ku dauko wannan Application mai suna PHOTOMATHS.
Download Photo Maths.apk
Bayan kunyi download na wannan application, sai kuyi install dinsa sannan ku budeshi da zarar kun bude saiku duba daga samansa akwai wasu alamomi, to saiku shiga Alamar Camera, da zarar kun shiga zai baku damar daukan tambayar, da kukeso ku, to saiku dauko Littafi ko wani takarda, saiku Rubuta tambayar/lissafin ajiki, sannan saiku haska da wannan application, hmm da zarar kun haska idan ta gama scanning nan take zakuga ta baku amsa, insha Allah. . Allah ya bada sa,a .