
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,
Dayake jawabi shugaban kungiyar yayi kira ga yan Kwamitin da su tsaya tsayin daka Kamar yadda suka saba domin ganin aikin ya kammalu cikin nasarar Ubangiji, Haka Al'umma kasar Nigeria dasu bayar da gudumawarsu na fatun layya domin ciyadda addini gaba.
Dayake jawabi Sakataren kungiyar ta kasa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya bayyana yadda akatafiyar da kudaden da akatara a shekarun baya wadda a bayyane suke ga Al'ummar da sukabayar da taimakonsu,
Shima Shugaban Kwamitin tattara fatun layya Sheikh Habibu Yahaya Kaura yayi kira ga yan Kwamitin na jihohi da su yi kokarin wajen ganin sun sauke nauyin da aka daura musu, kuma suyi aiki tukuru domin aikin yatafi yadda ake bukata.
Daga Karshe Shugaban Majalisar malamai ta kasa Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo yayi Addu'ar alkhair ga Al'umma dasuke bayar da fatun layyarsu domin ciyadda addini gaba
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da Kwamitin tattara fatun layya na Bana yau a Jihar Kano,An Rubuta Ranar 22/07/18
Category :-
Jibwis
,
LABARAI

0
Rate up
Star
Share: